Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade

Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade

- Uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai ta yi zazzafan martani ga danta a twitter

- Bello El-Rufai ya yi barazanar fyade ga mahaiifiyar wani wanda sabanin siyasa ya hada su a twitter din

- Jama'a sun fara caccakar uwargidan gwamnan bayan ta ce komai daidai ne soyayya da yaki

Uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai ta yi martani mai zafi ga danta a kan barazanar da yayi wa wani a twitter.

Matar gwamnan, wacce da farko aka fara caccaka a kan kare danta da tayi a ranar Lahadi, ta bada hakurin cewa sai daga baya ta karanta wallafar danta da kyau.

Daga nan ne ta zauna tare da tattaunawa da shi, sannan ta fahimci abinda ke faruwa.

Ta ce ba za ta goyi bayan cin zarafi ba kowanne iri kuwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin da muhawarar siyasa ta fara ne Bello El-Rufai ya bayyana gazawar shugaban kasar Amurka a yakar annobar Coronavirus.

Lamarin ya koma fada tsakaninsa da wani ma'abocin amfani da twitter din.

Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade
Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaban kasar Chadi ya caccaki gwamnatin Najeriya a kan sakin 'yan Boko Haram (Bidiyo)

Abokin fadan ya ce Trump ya fi shugaban kasa Muhammadu Buhari kokari da kuma mahaifin Bello, Gwamna Nasir El-Rufai.

Bello ya mayar da martani inda yake cewa: "Ka sanar da mahaifiyarka zan mika ta ga abokaina da daren nan".

Masu amfani da kafar sada zumuntar sun fara jawo hankalin matar gwamnan ga wallafar da danta yayi.

Ta ce: "Duk masu magana a kan Bello El-Rufai, su daina ambatona. Abinda ka shuka, shi za ka girbe. Komai daidai ne a soyayya da yaki. Ka mutunta kowa amma kada ka amince a taka ka. Ban ga wata barazanar fyade ba."

Amma daga bisani sai uwargidan gwamnan ta wallafa: "A lokacin da nayi wannan rubutun, a zatona fadan da aka saba yi ne a twitter. Na tattauna da Bello. Kada ya sake amfani da barazanar fyade a matsayin makamin yaki"

Ta kara da cewa, "Na ga yadda wallafata ta yadu kuma ina bada hakuri ga wadanda ransu ya baci. Ina kara jaddada cewa, ba zan goyi bayan cin zarafi ba kowanne iri kuwa".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel