Gwamnatin Borno Ta Yi Sabuwar Hubbasa a Yunkurin Kawo Karshen 'Yan Ta'adda
- Gwamnatin Borno ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum ta ba da ƙarin kayan aiki ga rundunar sojojin Najeriya
- Farfesa Zulum ya ba da motoci da babura ga sojoji waɗanda ke aikin samar da tsaro a ƙaramar hukumar Dikwa da ke jihar
- Zulum ya kuma yabawa sojojin kan goyon bayan da suke bayarwa wajen sake tsugunar da mutane ƴan gudun hijira a Dikwa da kewaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnatin Borno ta ba da gudummawar motocin aiki guda biyar da babura 15 ga rundunar sojojin Najeriya.
Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum ta ba da motocin ne domin inganta ayyukan tsaro a ƙaramar hukumar Dikwa.
Zulum ya ba jami'an tsaro kayan aiki
Gwamna Babagana Zulum ne ya bayar da kayan aikin a ranar Litinin, yayin wata ziyara da ya kai wa runduna ta 24 ta sojojin Najeriya da ke Dikwa, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Zulum, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar, Dr Umar Kadafur, ya jaddada muhimmancin samar da kayan aiki ga jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Zulum ya ce biyu daga cikin motocin guda biyar na rundunar CJTF ne yayin da sauran guda ukun na sojoji ne, rahoton gazettengr ya tabbatar.
Gwamnatin Zulum ta yabawa sojoji
Gwamnan ya yabawa kwamandan rundunar, Birgediya Janar Ezekiel Bawa Barkins, saboda goyon bayan da sojoji suke bayarwa wajen tabbatar da samun nasarar sake tsugunar da ƴan gudun hijira a Dikwa da kewaye.
Ya kuma buƙaci jami’an tsaro da su sanya ido tare da ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Ya ce bayar da kayan aikin na daga cikin ƙoƙarin da gwamnati take yi wajen nuna goyon baya ga jami'an sojoji da ƴan banga, a yaƙin da suke yi da masu tayar da ƙayar baya.
Zulum ya yi fallasa kan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wani zargi kan rikicin ƴan ta'addan Boko Haram.
Gwamna Zulum ya yi zargin cewa waɗanda ba su son rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ya ƙare, su ne masu amfana da zubar da jinin da ake yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng