Gwamnatin Tinubu Ta Fito da Ainihin Bayani kan Naɗa Jakadu a Ƙasashen Waje
- Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta musanta aika jakadu ƙasashen waje tun bayan dawo da su gida a 2023
- Muƙaddashin jami'in hulɗa da jama'a na ma'aikatar harkokin ƙasashen waje, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya fadi haka
- Ya ce babu ƙamshin gaskiya a labarin cewa gwamnati ta naɗa sababbin jakadu zuwa ƙasashe daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana samun labarin jerin sunayen da ke yawo a matsayin sunayen jakadun da ta aika kasashen waje.
Ma'aikatar harkokin ƙasashen ta yi martani ga jerin sunayen, inda ta bayyana cewa har yanzu gwamnati ba ta naɗa jakadun da za su wakilce ta ba.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa muƙaddashin jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ne ya tabbatar da haka a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta magantu kan naɗa jakadu
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta shawarci jama'a da su yi watsi da sunayen da ake cewa su ne waɗanda ta naɗa a matsayin jakadu.
Wannan na zuwa bayan shugaba Bola Tinubu ya dawo da dukkanin jakadun ƙasar nan da ke waje bayan hawansa mulki a shekarar 2023, kuma har yanzu ba a naɗa wasu ba.
"Tinubu ne zai naɗa jakadu," Gwamnati
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kaɗai ke da ikon naɗa jakadun da za su wakilci ƙasar nan a ƙasashen waje.
Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya ƙara da cewa;
"Ma’aikatar (ƙasashen waje) na son bayyana cewa nadin jakadu hakki ne na shugaban ƙasa, kuma ya zuwa yanzu ba a yi wannan naɗe-naɗe ba."
Shugaba Tinubu ya dawo da dukkanin jakadu
A wani labarin, mun ruwaito cewa jim kaɗan bayan hawansa mulkin ƙasar nan, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkanin jakadun Najeriya su dawo gida a watan Oktoba.

Kara karanta wannan
Gwamna da 'yan tawagarsa sun yi batan hanya, sun tsinci kansu a tsakiyar 'yan ta'adda
Yusuf Tuggar, Ministan Harkokin Waje, da ya sanar da matakin, ya kara da cewa umarnin ya shafi dukkanin jakadu da ke wakiltar Najeriya a ƙasashen duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng