Ana cikin halin wahala, Gwamna zai cika kasuwanni da shinkafa mai rahusa
- Yayin da yan Najeriya ke cigaba da kokawa kan halin da ake ciki, Gwamnatin Lagos ta dauko hanyar dakile hakan
- Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya shirya samar da shinkafa a kasuwannin jihar domin karya farashi
- Wannan na zuwa ne yayin da farashin kayan abinci ke kara tsada a Najeriya hade da na man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Gwamnatin Lagos ta nemo hanyar dakile tsadar abinci musamman shinkafa jihar.
Gwamnatin ta yi alkawarin cika kasuwanni da shinkafar kamfanin Eko cikin mako daya zuwa biyu masu zuwa.
Gwamna Sanwo-Olu zai wadata kasuwanni da shinkafa
Kwamishinar harkokin noma, Abisola Olusanya ita tabbatar da haka yayin taron al'adu da abinci, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olusanya ta ce Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi hakan ne domin tabbatar da samun damar siyan shinkafa mai inganci a farashi mai rahusa.
A cewarta, za a kara yawan shinkafar da ake sarrafawa a kamfanin shinkafa ta Lagos.
Ta kara da cewa hakan zai tabbatar da cewa mazauna jihar da ke bukatar shinkafa a kan farashi mai rahusa sun samu.
Har ila yau, Olusanya ta bayyana cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayar da kulawa ta musamman wajen sayen karin shinkafar da ba a sarrafa ba.
Gwamna Sanwo-Olu ya karfafi masu sarrafa shinkafa
Olusanya ta ce hakam zai kara karfafa matatar shinkafa wajen samar da karin kayan abinci ga mazauna jihar.
Rahotanni sun tabbatar cewa gwamnatin jihar na aiki tukuru wajen rage farashin abinci a bangarori daban-daban.
Gwamnatin tana yin haka domin tabbatar da cewa masu ruwa da tsaki sun karfafa yawan samar da kayayyakin masarufi.
Farashin abinci ya sauka a Ondo
Kun ji cewa rahotanni sun tabbatar cewa sauƙi ya zo a birnin Akure na jihar Ondo yayin da farashin kayayyakin abinci ya yi ƙasa sosai a kasuwa.
Buhun kwaki ya zaftare N20,000 daga farashin da ake sayar da shi a baya na N55,000 inda ya koma N35,000 yanzu.
Taliya, shinkafa da wake duk sun yi ƙasa, yayin da farashin manja da tattasai suka yi tashin gwauron zabi.
Asali: Legit.ng