'Yan Sanda Sun Yi Bajinta, Sun Tsallake Cin Hancin $17,000 daga Hannun 'Yan Damfara
- Jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Rivers sun kawar da kai kan cin hancin maƙudan kuɗaɗe da aka ba su
- Ƴan sandan sun ƙi karɓar cin hancin $17.000 da wasu masu damfarar yanar gizo suka ba su bayan an cafke su
- Mutanen dai sun yi fice wajen shirya damfarar yanar gizo wacce suka daɗe suna tatsar ƴan ƙasashen waje da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Rundunar ƴan sanda da ke shiyya ta 16 a jihar Bayelsa, ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da laifin damfarar yanar gizo da samun haramtattun ƙwayoyi.
Ƴan sandan sun ce waɗanda ake zargin su ne Billion Ndubuisi, Charles Amachree, da Martins Chinemike.

Source: Twitter
Ƴan sanda sun cafke masu laifi a Rivers
A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, Gunn Emonena, mai magana da yawun rundunar shiyya ta 16, ya tabbatar da kamen, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an cafke waɗanda ake zargin ne a ƙauyen Rumukparali, ƙaramar hukumar Obio/Akpo a jihar Ribas bayan da jami’an ƴan sanda suka yi aiki da sahihan bayanan sirri, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Gunn Emonena ya ce ƴan sanda sun ƙwato ƙunshin haramtattun ƙwayoyi da ake zargin wiwi ce, motoci biyu, kwamfutoci biyu da wayoyi 10 yayin binciken harabar gidan waɗanda ake zargin.
Ƴan sanda sun ƙi karɓar cin hanci
Kakakin ƴan sandan ya ce waɗanda ake zargin sun ba jami’an cin hancin dala 17,000 domin su boye laifin amma ba su karɓa ba.
"Waɗanda ake zargin ta hannun wakilinsu sun bayar da cin hancin Dala 17,000 amma ƙwararrun jami’anmu ba su karɓa ba."
- Gunn Emonena
Kakakin ƴan sandan ya ce waɗanda ake zargin sun amsa laifin yi wa wani ɗan ƙasar Amurka, Ryan Bill, sojan gona wajen damfarar ƴan ƙasashen waje kuɗi dala 71,500.
Ɗan sanda ya harbi ƴar uwar gwamna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jami'in ɗan sanda ya harbi ƴar uwar gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, mai suna Atsi Kefas.
Jami'in ɗan sandan ya yi harbin ne bisa kuskure lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai musu hari a ranar Alhamis, 5 ga watan Disamban 2024.
Asali: Legit.ng

