'Yan Bindiga Sun Farmaki Kauyuka, Sun Hallaka Mutum 8, Sun Sace Mutane Masu Yawa

'Yan Bindiga Sun Farmaki Kauyuka, Sun Hallaka Mutum 8, Sun Sace Mutane Masu Yawa

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-hare a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Kankara da ke jihar Katsina
  • Miyagun a yayin hare-haren sun hallaka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba sannan suka yi garkuwa da wasu masu yawa
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a tsakanin ranakun Juma'a da Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Wasu ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Kankara da ke jihar Katsina.

Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka mutane takwas tare da raunata wasu da dama, sannan suka yi garkuwa da wasu mutane masu yawa.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina Hoto: Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Majiyoyi sun shaidawa jaridar Vanguard cewa ƴan bindigan sun kai hare-haren ne tsakanin ranakun Juma'a da Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

"Da sanyin safiyar Asabar ƴan bindigan sun tafi da wata mota cike da mutane, kuma sun ƙara tafiya da wata motar cike da mutane."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi bajinta, sun tsallake cin hancin $17,000 daga hannun 'yan damfara

"Domin guje wa waɗannnan miyagu marasa tausayi, da yawa daga cikin mutanen ƙauyukan sun gudu zuwa cikin daji, kuma an kashe wasu daga cikinsu a ƙoƙarin yin hakan."

- Wata majiya

Ƴan bindigan sun kai mutanen da suka yi garkuwa da su zuwa maboyarsu yayin da da yawa daga cikin mazauna ƙauyukan suka ci gaba da tserewa domin tsira da rayukansu.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa ƴan bindigar a hare-haren sun farmaki ƙauyuka da dama a yankin.

Majiyar ta alaƙanta kai harin kan wani shugaban ƴan bindiga, wanda aka bayyana sunansa da Bambara na Gidan Gamji.

A cewar majiyar, ɗan bindigan yana da iko a yankunan Pauwa, Jeka, da Masalawa.

Idris Hussain ya shaidawa Legit Hausa cewa ƴan bindigan sun kai harin nw a ƙauyen Ɗan Murabu da ke yankin Arewacin Kankara.

"Eh an kai hari a ƙauyen Ɗan Murabu, kuma ƴan bindigan sun kashe mutane tare da sace wasu da dama."

Kara karanta wannan

An samu asarar rai bayan barkewar rikici tsakanin matasa da makiyaya a Arewa

- Idris Hussain

Ba a ji ta bakin ƴan sanda ba

Ƙoƙarin da Legit Hausa ta yi domin jin ta bakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, kan aukuwar harin ya ci tura.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa sannan ba bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun sace likita

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun sace wani kwararren likita, Dr. Donatus Nwasor a kauyen Utagba-Uno, ƙaramar hukumar Ndokwa ta Yamma a jihar Delta.

Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun kutsa cikin asibitin likitan na kudi, inda suka sace shi da misalin ƙarfe 8:15 na daren ranar Talata, 26 ga watan Nuwamban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng