Dattawan Arewa Sun Gindaya Sharuda ga Tinubu domin Janye Adawarsu kan Kudirin Haraji
- Manyan kungiyoyin dattawa da matasan Arewa sun magantu kan sharudan janye adawarsu kan kudirin haraji
- Kungiyoyin sun kawo sharuda na musamman ga gwamnati domin duba yiwuwar daukar matakai kan kudirin
- Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da korafe-korafe kan kudirin haraji musamman daga yankin Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Ana cigaba da adawa daga Arewacin Najeriya kan sabon kudirin haraji da ke gaban Majalisar Tarayya.
Wasu manyan kungiyoyi a yankin Arewa sun gabatar da sharuddan da dole a bi kafin daina adawa da kudirorin.
Kudirin haraji: Dattawan Arewa sun ba Tinubu shawara
Vanguard ta ce kungiyoyin sun dage cewa adawarsu ta dogara ne kan yadda gyare-gyaren ke iya shafar yanayin tattalin arziki na Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dattawan Arewa sun bukaci gwamnati ta yi alkawarin magance rashin daidaito da suka ce ya kawo cikas ga cigaban yankin.
Haka kuma, sun jaddada bukatar bin ka’idojin gaskiya da adalci da fadada tattaunawa da gina amana kafin su marawa kudirorin baya.
Kungiyoyin Arewa, Northern Elders Forum (NEF) da Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) da Arewa Consultative Forum (ACF) sun ce ba za su daina adawa ba idan ba a cika sharuddansu ba.
Dattawan Arewa sun gindaya sharuda kan kudirin haraji
Mai magana da yawun NEF, Abdul-Azeez Suleiman ya ce dakatar da adawar ba zai wadatar ba matukar ba a dauki matakan da suka dace ba.
Matakan sun hada da magance matsalolin da suka haddasa rashin jituwa ba tare da gina amana tsakanin gwamnati da yankin.
“A ra’ayina, samun zaman lafiya kan takaddamar da ta taso game da kudirorin gyaran harajin Tinubu abu ne mai yiwuwa."
"Amma sai an dauki matakan tattaunawa na gaskiya da hadin kai domin kawo daidaito a tsakani.”
- Abdul-Azeez Suleiman
Tsohon gwamna ya magantu kan kudirin haraji
Kun ji cewa, tsohon gwamnan jihar Niger, Mu'azu Babangida Aliyu ya caccaki masu sukar sabon kudirin haraji.
Babangida Aliyu ya ce mafi yawan masu korafi kan kudirin harajin ba su ma karanta ba bare su san abin da ke ciki.
Asali: Legit.ng