Bayanai Sun Fito kan 'Dalilin' Mamaye Fadar Sanusi II, An Ce Hakan Ka Iya Zama Alheri
- An samu bayanai kan ainihin dalilin sanya jami'an tsaro mamaye fadar Sarki Muhammadu Sanusi II a jihar Kano
- Rahotanni sun ce jami'an tsaro sun samu bayanan sirri cewa yan garin Bichi na shirin wargaza bikin nadin hakimi a garin
- Hakan bai rasa nasaba da zargin Abba Kabir da ragewa masarautar Bichi daraja yayin da ya dawo da sauran masarautu darajarsu da aka rusa su tare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Wasu bayanai sun bayyana kan dalilan rufe kofar shiga fadar Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a ranar Juma'a.
Duk da cewa rundunar ‘yan sanda ba ta yi karin bayani ba, wata majiya mai tushe ta bayyana dalilin matakin da jami’an tsaro suka dauka na mamaye fadar.
Rahotanni sun fadi musabbabin mamaye fadar Sanusi II
Jaridar Tribune ta ce majiyoyi sun tabbatar hakan na nufin dakile tashin hankalin da ka iya barkewa a garin Bichi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya, wadda ta nemi a sakaya sunanta ta ce mazauna garin Bichi sun shirya tsaf don hana wannan nadin ya gudana a garinsu.
Sai dai bayanan da jami’an tsaro suka samu shi ya tilasta daukar matakin gaggawa domin hana Sarkin Kano halartar taron.
Wasu rahotanni sun ce da yawa daga mazauna garin Bichi ba su ji dadin shirye-shiryen nadin ba, inda suke tambayar dalilin da ya sa za a nada hakimi a garin.
Wasu daga cikin mazauna garin sun bayyana cewa shirye-shiryen nadin hakimin na nufin rage darajar Bichi.
Zargin Abba Kabir da rage darajar masarautar Bichi
A cewarsu, bayan Abba Kabir Yusuf ya rushe masarautu, ya nada sarakuna masu na daraja ta biyu ga wasu daga cikin masarautun da aka rushe, amma bai hada da Bichi ba.
Hakan bai rasa nasaba da zargin gwamnan na rage darajar masarautarsu ta koma karkashin hakimi idan aka kwatanta da sauran da ke karkashin sarakunan.
Har ila yau, masu ruwa da tsaki sun ce matakin da 'yan sanda suka dauka ka iya zama alheri domin hana barkewar rikici a garin Bichi, wanda ka iya shafar sauran al'ummomi a jihar.
Hankula sun kwanta a Kano bayan rigimar sarauta
Kun ji cewa rahotanni sun tabbatar da cewa lamura sun koma yadda suke bayan janye jami'an tsaro a fadar Sarki Muhammadu Sanusi II.
Da safiyar jiya Asabar 7 ga watan Disambar 2024 komai ya dawo yadda yake bayan arangama a ranar Juma'a kan rigimar sarauta a birnin Kano.
Asali: Legit.ng