Halin da Ake Ciki a Kano bayan An Hana Sarki Sanusi II Fita, An Janye Jami'an Tsaro

Halin da Ake Ciki a Kano bayan An Hana Sarki Sanusi II Fita, An Janye Jami'an Tsaro

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa lamura sun koma yadda suke bayan janye jami'an tsaro a fadar Sarki Muhammadu Sanusi II
  • Da safiyar yau Asabar 7 ga watan Disambar 2024 komai ya dawo yadda yake bayan arangama a jiya Juma'a kan rigimar sarauta a birnin Kano
  • Wannan na zuwa ne bayan sabuwar rigimar sarauta ta barke da aka hana Sanusi II zuwa nadin hakimin Bichi a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - An samu zaman lafiya a birnin Kano a yau Asabar 7 ga watan Disambar 2024 bayan rigimar sarauta a jiya Juma'a.

Hakan ya biyo bayan janye jami’an tsaro dauke makamai da kuma motocin masu sulke a fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

An janye jami'an tsaro da suka mamaye fadar Sarkin Kano
An samu kwanciyar hankali a Kano a yau Asabar bayan janye jami'an tsaro a fadar Sarki Sanusi II. Hoto: @masarautarkano.
Asali: Twitter

Hakin da ake ciki a Kano bayan rigimar sarauta

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi martani yayin da jami'an tsaro suka mamaye fadar sarkin Kano

Leadership ta ruwaito cewa an samu kwanciyar hankali kuma komai ya koma kamar yadda yake da aka janye jami'an tsaro wanda ya tayar da hankulan al’umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan kai ruwa rana a jiya Juma'a 6 ga watan Disambar 2024 bayan jami'an tsaro sun mamaye fadar Sarki Muhammadu Sanusi II.

Lamarin ya faru ne yayin da basaraken ya shirya halartar bikin nadin sarautar sabon hakimin Bichi a jihar.

An yi koƙarin jin ta bakin yan sanda

Sai dai duk da kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano kan dalilin janye jami'an tsaron game da lamarin ya ci tura.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar bai amsa kira ko sakonnin da ‘yan jarida suka tura masa ba.

Duk da haka wasu na rade-radin cewa matakin na da nasaba da umarni daga sama watau Gwamnatin Tarayya.

Sanusi II ya yi martani kan rigimar sarauta

A baya, kun ji cewa Sarki Sanusi II yayin hudubar Sallar Juma'a ya yi martani kan wannan mamayar inda ya ce wasu ne ke neman tayar da fitina a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Ana cikin rigimar sarauta, Sanata Kashim Shettima ya dira jihar Kano a yau Juma'a

Mai martaban ya yi kira ga mazauna Kano da su guji rikici, yana mai cewa haƙuri shi ne mafita ga duk wata fitina da ake ƙoƙarin tayarwa saboda kawo tsaiko.

Wannan kira na basaraken ya zo a daidai lokacin da jami'an tsaro suka kewaye fadarsa a kokarin hana shi zuwa bikin nadin sarautar hakimin Bichi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.