Albashin N70,000: Rikici Ya Balle Tsakanin PDP Da ’Yan Kwadago a Jihar Kebbi Game da Albashi
- Kunfiyar Kwadago a jihar Kebbi ta yiwa jam’iyyar PDP wankin babban bargo kan batutuwan da suka shafi albashin ma’aikata
- Jam’iyyar PDP ta zargi rashin daidaito wajen aiwatar da tsarin albashin da gwamnati ta amince dashi, ta bayyan hujojinta
- Tun bayan mayar da mafi karancin albashin N70,000 a Najeriya ake samun gwamnonin da ke aiwatar da hakan a jihohinsu
Jihar Kebbi - Reshen Kebbi na Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ya yi kakkausan suka ga jam’iyyar adawa ta PDP kan matsayinta a batun aiwatar da sabon mafi karancin albashi na Naira 75,000 ga ma’aikatan kananan hukumomi a jihar.
Shugaban NLC na jihar, Murtala Usman, ya bayyana cewa kungiyar kwadago aikinta shi ne kare walwala da jin dadin ma’aikata, ba wakiltar gwamnati ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Murtala ya bukaci a rika yin tattaunawa mai ma’ana kan batutuwa ba wai magana sakaka ba, rahoton Punch.
Ya ce:
“Walwalar ma’aikatan kananan hukumomi abu ne mai matukar muhimmanci. Su ne ginshikin al’umma, don haka jin dadinsu ya kamata ya kasance muhimmin abu ga kowa.”
NLC ta yabawa gwamnan Kebbi
Murtala ya yabawa Gwamna Nasiru Idris bisa gaggawar da ya yi wajen aiwatar da sabon tsarin albashin bayan amincewar Gwamnatin Tarayya.
Ya ce gwamnan ya shiga cikin jerin ’yan tsirarun gwamnoni da suka dauki wannan matakin nan take, wanda hakan ya taimaka wajen inganta rayuwar ma’aikata.
Haka kuma, ya kara da cewa gwamnan na kokarin aiwatar da wasu shirye-shirye na musamman domin inganta yanayin aiki da jin dadin ma’aikata a jihar.
Akwai sarkakiya wajen ba da albashi a Kebbi
Ya bayyana cewa baya ga wannan sabon albashi, an sha samun matsaloli a baya wajen aiwatar da karin albashi kamar na N18,000 da N30,000, wadanda ba su taba kai wa ga ma’aikatan kananan hukumomi ba.
NLC ta bukaci PDP da ta hada hannu da gwamnatin wajen kokarin inganta yanayin ma’aikatan, maimakon yin suka ba tare da samar da wata mafita ba.
A cewar Murtala:
“Ta hanyar hadin kai, za mu iya gina tsarin ci gaba da kyautata walwalar ma’aikata don amfanin al’ummarmu baki daya.”
Abin da PDP ke cewa kan albashin Kebbi
Sai dai PDP ta yi zargin cewa akwai bambance-bambance a aiwatar da sabon albashi, tana cewa wasu ma’aikatan kananan hukumomi da malamai na karbar kasa da N75,000 da aka tsara.
Kakakin PDP, Alhaji Sani Dododo, ya tuhumi dalilin da ya sa ake samun nau’ikan albashi daban-daban a jihar. Ya yi ikirarin cewa ma’aikatan matakan GL 3, 4, da 5 har yanzu na karbar kasa da N40,000.
Dododo ya kuma zargi gwamnatin jihar da fifita mukaman siyasa fiye da batun ilimi da ci gaban al’ummomi, rahoton Channels Tv.
Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnatin jihar da ta cika alkawuran da ta dauka ga malamai, tana mai cewa malamai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina makomar al’umma, don haka jin dadinsu ya kamata ya zama babban abin mai da hakali.
Gwamna Sule ya tabbatar da mafi karancin albashi
A wani labarin, kun ji yadda gwamnan jihar Nasarawa ya tabbatar da aiwatar da sabon mafi karancin albashi na Najeriya.
Ya shiga jerin gwamnonin da suka amince su biya ma'aikata akalla N70,000 a matsayin albashi a Najeriya.
Wannan albashi dai bai taka kara ya karya ba, domin har yanzu 'yan Najeriya na kukan ba zai ishe su rike gida ba.
Asali: Legit.ng