Gwamna da 'Yan Tawagarsa Sun Yi Batan Hanya, Sun Tsinci Kansu a Tsakiyar 'Yan Ta'adda
- Gwamnan jihar Neja tare da ƴan tawagarsa sun yi ɓatan hanya lokacin da suke rangadin duba ayyuka a shiyyar Neja ta Arewa
- Majiyoyi da dama sun bayyana cewa tawagar ta tsinci kanta a wuraren da ƴan ta'adda ke da iko inda aka yi musayar wuta
- Sai dai, gwamnatin jihar ta musanta aukuwar lamarin inda ta ce babu wani abu makamancin hakan da ya auku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago da tawagarsa sun tsinci kansu a wurin da ƴan ta'adda ke da iko a ranar Lahadin da ta gabata.
Gwamna Bago tare da ƴan tawagarsa sun yi ɓatan hanya ne inda suka tsinci kansu a maɓoyar ƴan ta'adda a yankin Igade a ƙaramar hukuma Mashegu da Bangi na ƙaramar hukumar Mariga.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa gwamnan yana yin rangandi ne a shiyyar mazaɓar sanatan Neja ta Arewa, domin duba ayyukan da ake yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda tawagar Gwamna Bago ta je maɓoyar ƴan ta'adda
Majiyoyi da dama ciki har da waɗanda ke kusa da ƴan tawagar gwamnan, sun shaidawa jaridar cewa, iftila'i ya kusa faɗa musu lokacin da suka tsinci kansu a wuraren da ƴan ta'adda ke da mafaka a yayin da suka nufi Kontagora.
"Sun yi ɓatan hanya ne inda suka tsinci kansu a yankin Bangi da Igade wanda ne ƙarƙashin ikon ƴan bindiga."
- Wata majiya
Wata majiya ta kusa da gwamnati ta bayyana cewa jami'an tsaron da ke tattare da tawagar sun gano cewa yankin bai da tsaro inda suka ba da shawarar su juyo baya.
"A lokacin da suke ƙoƙarin juyowa ne su bi wata hanyar, sai ƴan bindigan suka buɗe musu wuta. Amma jami'an tsaro sun fatattake su."
- Wata majiya
Majiyar ta kuma yi iƙirarin cewa jami'an tsaron sun hallaka wasu daga cikin ƴan ta'addan, yayin da sauran suka koma cikin daji.
Gwamnati ta musanta aukuwar lamarin
Sai dai gwamnatin jihar Neja ta bakin sakataren yaɗa labaran gwamna, Ibrahim Bologi, ta musanta aukuwar lamarin.
Ibrahim Bologi a wata sanarwa a shafinsa na X ya bayyana labarin a matsayin na ƙarya, inda ya ƙara da cewa babu abin da ya samu gwamnan da ƴan tawagarsa a lokacin rangadin.
An cafke ɗan jarida a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta cafke wani ɗan jarida mai suna Mustapha Bina, wanda ke aiki da jaridar People’s Daily a jihar Neja.
An cafke ɗan jaridar ne bayan ya ba da rahoto kan harin ƴan bindiga da aka ce sun kai wa tawagar Gwamna Muhammed Umaru Bago a ƙaramar hukumar Mashegu.
Asali: Legit.ng