"Har Yanzu Najeriya na cikin Matsala," CBN Ya Yi Magana kan Tattalin Arziki
- Babban baki watau CBN ya tabbatar da cewa har yanzun Najeriya na fama da matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki
- Gwamnan CBN, Yemi Cardoso ya ce ma'aikatan banki na da matuƙar muhimmanci wajen magance kalubalen da ƙasa fuskanta
- Ya ce Najeriya na bukatar magance talauci, hauhawar farashin kayayyaki, rashin tsaro, zaman kashe wando da dai sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya watau CBN, Yemi Cardoso ya ce har yanzun Najeriya na fama da matsalar kuɗi da tattalin arziki.
Cardoso ya fito ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron shekara-shekara na kwamitin ma’aikatan banki karo na 14 a Abuja.
Ya bayyana cewa aikin kwamitin ma’aikatan banki na da matukar muhimmanci wajen tunkarar kalubalen tare da daidaita tattalin arziki, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan CBN ya jero wasu ƙalubalen Najeriya
Gwamnan CBN ya ce Najeriya na fuskantar kalubale kan yadda za ta magance talauci, hauhawar farashin kayayyaki, karancin ababen more rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi da dai sauransu.
Ya yi kira ga mambobin kwamitin ma’aikatan banki da su yi tunani a kan kalubalen da aka fuskanta a bara tare lalubo hanyar magance su.
Hadimin Tinubu ya roki CBN, bankuna
A nasa bangaren, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, Tope Fasua, ya nuna damuwarsa kan tsadar cire kudi a wurin masu POS.
Ya buƙaci babban bankin Najeriya da bankunan kasuwanci su samar da isassun kuɗaɗe a na'urorin cire kudi watau ATMs domin rage wahala ga ƴan Najeriya.
Taron wanda ya ɗauki tsawon kwanaki uku ya haɗa manyan masana da masu ruwa da tsaki a harkokin banki da hada-hadar kudi.
CBN ya kare kansa kan shirin ritayar wuri
Kuna da labarin babban baki CBN ya ƙarin haske kan shiirinsa na rabawa ma'aikatansa 1000 da suka shirya ajiye aiki da wuri Naira biliyan 50.
CBN ya yi wannan bayani ne a matsayin martani ga majalisar wakilai, wadda ta umarci dakatar da dhirin ritaysr m'aikatan.
Asali: Legit.ng