Bola Tinubu Ya Yi Amai Ya Lashe kan Naɗin Sabon Shugaban SMDF, Ya Dawo da Mace
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sabunta naɗin Fatima Umaru Shinkafi a matsayin shugabar SMDF/PAGMI
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya ce an soke naɗin da aka yi wa Yazid Shehu Ɗanfulani saboda babu gurbi
- Ya ce tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Fatima a wannan matsayi kuma ta taka rawar gani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya canza shawara game ɗa naɗin shugaban asusun kula da harkokin haƙar ma'adanai watau SMDF/PAGMI.
Mai girma Shugaba Tinubu ya soke naɗin Yazid Shehu Danfulani a matsayin wanda zai shugabanci SMDF/PAGMI, ya ce babu wurin da za a naɗa wani a hukumar.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mashawarcin shugaban kasa kan harkokin yaɗa labaru da dabaru, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya soke naɗi cikin awanni
An yi wa sanarwar taken, "Shugaba Tinubu ya yi naɗe-naɗen shugabanni a NUC, NERDC, NEPAD, ya sabunta naɗin Fatima Shinkafi a SMDF.”
Sanarwar ta ce Tinubu soke nadin Yazid Danfulani ne saboda "babu wani gurbi a hukumar," inda ta mayar da Fatima Shinkafi a matsayin shugabar hukumar karo na biyu.
A cewar Onanuga, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fara nada Fatima kuma Bola Tinubu ya gamsu da gogewarta, ya kara mata dama a karo na biyu.
Tinubu ya sabun naɗin Fatima Shinkafi
"Shugaban ƙasa ya kuma amince da sabunta nadin Fatima Umaru Shinkafi a matsayin shugabar asusun bunkasa harkokin ma'adanai watau SMDF/PAGMI.
"Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ne ya fara nada ta a wannan aiki kuma an ce tana daya daga cikin masu kawo sauye-sauye a fannin ma’adinai.
"An soke naɗin farko na Yazid Shehu Umar Danfulani a matsayin shugaban SMDF/PAGMI saboda babu wani gurbi a hukumar.”
- Bayo Onanuga.
Shugaba Tinubu ya yi rabon muƙamai
A wani rahoton, an ji cewa Shugaba Tinubu ya yi sauye-sauye a hukumar raya Arewa maso Yamma watau NWDC, ya naɗa shugaganni a SEDC.
Shugaban ƙasar ya miƙa sunayen waɗanda yake son su jagoranci hukumomin guda biyu ga majalisar dattawan Najeriya domin tantancewa.
Asali: Legit.ng