'Dan Sanda Ya Harbi 'Yar Uwar Gwamna, An Gano Abin da Ya Faru
- Ƴan bindiga sun farmaki iyalan gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas a ranar Alhamis, 5 ga watan Disamban 2024
- Wani jami'in ɗan sanda ya harbi ƴar uwar gwamnan bisa kuskure a ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kai
- Jami'an sojoji sun kawo musu agajin gaggawa, suka yi nasarar korar ƴan bindigan, yayin da aka garzaya da ƴar uwar gwamnan zuwa asibiti domin ba ta kulawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Wani jami'in ɗan sanda ya harbi ƴar uwar gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, mai suna Atsi Kefas.
Jami'in ɗan sandan ya yi harbin ne bisa kuskure lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai musu hari a ranar Alhamis.
Ɗan sanda ya harbi ƴar uwar Gwamna Kefas
A cewar Zagazola Makama, lamarin ya faru ne a kan titin Kente a ƙaramar hukumar Wukari ta jihar Taraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maihaifiyar gwamnan mai suna Jumai da Atsi suna cikin tafiya ne lokacin da ƴan bindiga suka yi musu kwanton ɓauna.
Ɗan sandan wanda yake ba da kariya ga iyalan, ya harbi Atsi bisa kuskure ne lokacin da yake ƙoƙarin daƙile harin ƴan bindigan.
Sojoji sun kai agajin gaggawa
Bayan kai harin, sojoji sun kawo ɗauki, inda suka ceto su tare da kwashe Jumai da Atsi Kefas daga wurin.
An garzaya da Atsi Kefas asibiti domin yi mata magani. Sai dai har yanzu ba a bayyana halin da take ciki ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Jami’an tsaro sun ƙwato motar da maharan suka yi amfani da ita. An kuma samu wata jigida da babu harsasai a cikinta da kayan fasinjoji a cikin motar.
Ƴan bindiga sun kai hari a Taraba
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari inda suka kashe wata ƴar kasuwa a unguwar Mayo Dasa da ke cikin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Jami'in hulɗa da jama'a na ƴan sandan jihar ya ce a lokacin da ƴan bindigan suka kutsa kai cikin gidan matar, sun yi amfani da adduna wajen karya tagar gidan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng