'Ina Jin Radadi': Bobrisky Ya Fadi Azabar da Yake Sha Idan Jinin Al'ada Ya Yanko Masa
- Fitaccen dan daudu a Najeriya, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya magantu game da samun bakon wata a jikinsa
- Bobrisky ya bayyana irin azabar da yake sha yayin da jinin ya zo masa inda ya ce hakan yana sanya jinsa cikakkiyar mace
- Dan daudun ya ce wani lokaci kamar ya yi kuka yake ji tsabar zafi da kuma radadi inda ya hakan na sauya masa tunani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Shahararren dan daudu a Najeriya, Idris Okuneye ya yi magana kan yadda yake ganin jinin al'ada.
Dan daudun da aka fi sani da Bobrisky ya bayyana wahalhalun da yake fuskanta yayin jinin al’ada inda ya ce yana shafar jikinsa da tunaninsa.
Bobrisky ya magantu kan zuwan jinin haila
Bobrisky ya bayyana haka ne a yau Juma'a 6 ga watan Disambar 2924 a shafinsa na Instagram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin rubutun, Bobrisky ya bayyana cewa radadin da yake ji lokacin al’adarsa yana sanya shi jin kansa tamkar cikakkiyar mace.
Dan daudun ya ce zafin da ke tattare da wannan lokaci yana sanya shi kuka saboda ba ya iya jurewa.
'Ina jin kaina tamlar cikakkiyar mace' - Bobrisky
“Gaskiya ina jin kai na a matsayin cikakkiyar mace, wani lokaci ina kuka idan na ga jini na saboda zafi mai tsanani.”
- Bobrisky
Wannan jawabin ya haifar da abin magana a kafafen sada zumunta inda wasu suka nuna masa goyon baya da tausayawa.
Sai dai wasu da dama sun nuna shakku kan gaskiyar abin da ya ke ikirari a matsayinsa na dan daudu, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
'Nonona yana mani ciwo' - Bobrisky
Kun ji cewa fitaccen dan daudun nan, Idris Okuneye ya kwana a wani asibiti da ke jihar Lagos saboda rashin lafiya ta gaggawa.
A ofishin yan sanda, dan daudun da aka fi sani da Bobrisky ya yi korafi kan wani irin ciwo da yake ji a cikin nonuwansa.
Hakan ya biyo bayan cafke Bobrisky da aka yi tare da kulle shi a ofishin yan sanda da ke Alagbon a jihar Legos.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng