Shugaba Tinubu Ya Kaɗu da Rasuwar Babban Malamin Addinin Musulunci a Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a yankin Yarbawa, Sheikh Muyideen Bello
- Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tsoron Allah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da addinin Musulunci
- Mai girma shugaban kasa ya buƙaci ƴan Najeriya su yi koyi da kyawawan halayensa na haƙuri, tausayi, juriya da ƙaunar zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi jimamin rasuwar Sheikh Muhyideen Ajani Bello, malamin da ya sadaukar da kansa wajen yi wa Musulunci hidima.
Sheikh Muyideen Bello, wanda ya rasu yana da shekaru 84 a duniya, ya shahara wajen wa'azi da jawo hankalin al'umma su bi tafarkin addinin Musulunci.
Bola Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai hazaka, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautar Allah da yada koyarwar Alkur’ani mai girma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na kunshe a wata sanarwar ta'aziyya da hadimin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai a dabaru, Bayo Onanuga ya fitar a shafin X ranar Juma'a.
Bola Tinubu ya yi alhinin rashin Shiekh Muyideen
Shugaba Tinubu ya faɗi wasu daga cikin halayen marigayin kamar ƙokarin tabbatar da zaman lafiya ta hanyar koyarwar addinin Musulunci.
Ya ce wa'azi da koyarwar marigayi Sheikh Muyideen Bello sun shiga lungu da saƙo a tsakanin al'ummar Musulmin Najeriya.
"Sheikh Bello mutum ne da ya sadaukar da kansa wajen karatu da koyarwa, wanda wa'azinsa ya yi tasiri a rayuwar mutane mara adadi," in ji Tinubu.
Shugaba Tinubu ya aika saƙon ta'aziyyar Muyideen
Shugaban ƙasa Tinubu ya yi addu'ar Allah ya gafartawa Sheikh Muyideen Bello kuma ya masa rahama, ya kuma miƙa sakon ta'aziyya ga iyalansa.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi koyi da halayen marigayi malamin ta hanyar yin adalci, tausayi, da sadaukar da kai, waɗanda kowa ya shaida a zamanin rayuwarsa.
Abubuwan sani game da Sheikh Muyideen
A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Muyideen Ajani Bello wanda aka haifa a Ibadan, jihar Oyo malami ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada addinin Musulunci.
Legit Hausa ta tattaro wasu muhimman abubuwa hudu da ya kamata ku sani game da marigayi Sheikh Muyideen wanda ya fi shekara 70 yana yin wa'azi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng