'Yan Najeriya Sun Yi Martani da Duniyar Musulunci Ta Yi Babban Rashin Malamin Addini
- A yau Juma'a 6 ga watan Disambar 2024 aka sanar da labarin rasuwar malamin Musulunci, Sheikh Muyidden Ajani Bello
- Malamin ya rasu ne yana da shekaru 84 a duniya inda al'umma da dama suka yabi halayensa na kirki da yake raye
- Daya daga cikin mabiyansa kuma mawakin addinin Musulunci shi ya fara sanar da rasuwar malamin a yau Juma'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Yan Najeriya da dama sun nuna alhini kan rasuwar babban malamin Musulunci a Najeriya.
Allah Madaukakin Sarki ya karbi rayuwar Sheikh Muyidden Bello a yau Juma'a 6 ga watan Disambar 2024.
An sanar da rasuwar Sheikh Muyidden Bello
Daga daga cikin mabiyansa, Alhaji Basit Olarenwaju shi ya fara sanar da rasuwar malamin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani, fitaccen malamin Musulunci, Alfa Aribidesi shi ma ya tabbatar da haka a lokacin hudubar sallar Juma'a a yau.
Bayan rasuwar marigayin, mutane da dama ciki har da malaman Musulunci da abokan arziki sun yi ta tura sakon ta'azziya.
Sun bayyana irin gudunmawar da malamin ya ba addinin Musulunci, suka ce za a yi kewarsa sosai.
Martanin mutane kan rasuwar Sheikh Muyidden Bello
Legit Hausa ta duba martanin da al'umma ke yi a shafin X bayan rasuwar malamin:
"Karshe ya zo, duk wani mai rai zai ya dandana zafin mutuwa kamar yadda Alkur'ani mai girma ya fada."
"Sheikh Ajani Bello ya hadu da Mahalliccinsa, Allah ya gafarta masa da kuma saka masa da gidan aljannar Firdausi."
"Allah ya maka rahama Sheikh Muyidden Ajani Bello, muryar da na fi jinya dadinta kan koyarwar Musulunci a faifan 'CD', Allah ya gafarta maka."
"Allah ya maka rahama Sheikh Muyidden Ajani Bello, mutum ne mai hikima kuma masani wanda ya fahimci al'adunmu."
"Ina mika sakon ta'azziya ga yan uwa Musulmai maza da mata da kuma iyalansa."
"Allah karbi bakuncin Sheikh Muyidden Ajani Bello, ya yafe masa ya haɗa shi da mutanen kirki."
"Inna Lillah wa inna illahi rajihun, Allah ya jikan Sheikh Muyidden Ajani Bello."
"Muna rokon Allah cikin rahamarsa ya gafarta masa ya yi masa rahama, muna rokon Allah ya karbi bakuncinsa ya haɗa shi da mutanen kirki albarkacin sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam."
Abubuwan sani game da Sheikh Muyidden Bello
Kun ji cewa Sheikh Muyideen Ajani Bello, wanda aka fi sani da "Baba Oniwasi Agbaye" ya riga mu gidan gaskiya a farkon Disamban nan.
Legit Hausa ta tattaro wasu muhimman abubuwa huɗu da ya kamata ku sani game da marigayi Sheikh Muyideen Ajani Bello.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng