Gwamnatin Kano Ta Yi Martani kan Mamaye Fadar Sarki Sanusi II
- Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta yi mamaki da ƴan sanda suka kewaye fadar mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II
- Sakataren gamnatin, Abdullahi Baffa ya ce sarki ya tsaya raka Wanban Kano zuwa yankinsa a garin Bichi amma ƴan sanda suka hana
- Ya ce suna zargin wasu tsirarun mutane da ke da ɗaurin gindi a Abuja ne suka kitsa lamarin domin tada zaune tsaye a jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnatin Kano karƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta nuna damuwa kan abin da ke faruwa a fadar mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce ta yi mamakin yadda aka wayi gari jami'an tsaro sun yi wa fadar sarki da ke Ƙofar Kudu kawanya.

Source: Facebook
Gwamnatin Kano ta faɗi waɗanda take zargi
A wata hira da tashar Freedom Radiyo, sakataren gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi ya ce suna zargin wasu mutane da suka samu ɗaurin gindi daga Abuja ne ke neman tada zaune tsaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce mai martaba sarki ya tsara raka Wamban Kano hakimin Bichi a yau Juma'a, inda zai yi sallah da zikirin Juma'a a can, kwatsam ƴan sanda suka hana.
Sarki Sanusi II ya shirya raka ɗansa Bichi
"Mai martaba ya shirya raka Wamban Kano hakimin Bichi, Munir Sanusi kasarsa kuma zai yi sallah da zikirin Juma'a a babban masallacin garin Bichi.
"Yau da safen nan muka tashi da wannan abin ban mamakin na ƴan sanda sun zo sun ce ba za a je ba, mun tambaya saboda menene, suka ce umarni aka ba su daga sama.
"To mun san dai an dain saukar da wahayi, don haka babu wata sama da za ta ba su umarni idan ba gwamnatin tarayya ba, koma waye ya bada wannan umarnin, mu zaman lafiya muke so."
- Dr. Abdullahi Baffa Bichi.
Gwamnatin Kano ba ta son tashin hankali
Bichi ya kuma tabbatarwa al'ummar jihar Kano cewa babu wani abin tashin hankali domin gwamnatin da suka zaɓa mai son zaman lafiya ce.
Abdullahi Baffa ya jaddada cewa Sarki Sanusi ba zai fasa raka Wamban Kano zuwa ƙasarsa ba kuma duk ranar da ya shirya za su raka shi.
Wani mazaunin Kano, Sanusi Sisiyaku ya shaidawa Legit Hausa cewa bai ji daɗin abin da ya faru a gidan sarki yau Juma'a ba kuma ba demokuraɗiyya ba ce.
Ya ce kamar yadda sakataren gwamnatin Kano ya faɗa, wasu ƴan siyasa da suka tare da a Abuja ne suke son haifar da tashin hankali tsakanin al'umma.
Sanusi ya ce:
"Na yi mamaki wallahi, tun jiya na samu labarin rakiyar da sarki zai yi wa Wamban Kano zuwa Bichi, ban taɓa kawo tunanin haka za ta faru ba
"Babu wani ɓoye-ɓoye mutanen Ganduje ne suka kitsa wannan lamarin, na rasa gane me suke nufi da Kano, ruguza mu suke son yi ko karaya tarihinmu?"
Yan sanda, SSS sun kewaye fadar Sanusi II
A wani labarin, kun ji cewa jami'an 'yan sanda da na SSS sun mamaye fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu.
An ruwaito cewa dakarun tsaron sun hana mutane shiga da fita daga fadar yayin da sarkin ke shirin yi wa sabon Wamban Kano, Munir Sanusi, rakiya zuwa masarautar Bichi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

