Ana Shirin Sallar Juma'a, Tagwayen Bama Bamai Sun Tarwatse a Ranar Kasuwa
- Wasu bama bamai guda uku sun fashe a jihar Zamfara, a lokacin da 'yan kasuwa ke shirin cin kasuwar Juma'a
- Wannan shi ne karo na uku da bam ya fashe kan titin da matafiya ke bi, lamarin da ke tsoaratar da jama'a
- Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin 'yan ta'addan sun dasa bama-bamai a yankin Maru da ke Dan Sadau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Jama'a a Zamfara sun shiga hargitsi bayan an sake samun tashin bama-bamai a wurare daban daban a jihar.
Lamarin ya afku a ranar Juma'a a garin Dan Sadau da ke karamar hukumar Maru, a lokacin da ake shirin gudanar da sallar Juma'a.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa bama-baman sun tashi a hanyoyin Dansadau da Malamawa da titin Malele duk a yankin Dan Sadau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bama bamai sun fashe a jihar Zamfara
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wannan shi ne karo na uku da bam ya fashe a Zamfara, wanda ya kara ta'azzara matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.
Wani mazaunin garin, Nuhu Babangida, ya bayyana cewa wasu fasinjoji sun taho wucewa kasuwar Juma'a da ke ci a garin a lokacin da bam ya tashi da su.
Zamfara: Masallata sun fuskanci harin bam
Har yanzu ba a samu cikakken rahoton samun rasa rayuka a harin bam da ya tashi a titunan Zamfara a ranar Juma'ar nan.
Sai dai an samu rahoton cewa, direban motar ya samu ya tsira da ransa bayan motar da ya dauko a makare da hatsi ya tarwatse.
Bama baman da su ka tashi a yankunan Malamawa da titin Malele ba su jawo asarar rayuka ba.
Bam ya tashi a kauyen Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa wani abu da ake zargin bam ne ya tashi a Zamfara, yayin da mutane akalla 12 su ka rasa rayukan a hanyarsu ta zuwa, a yankin Dan Sadau.
Jama'ar garin sun nemi daukin gwamnati domin dakile hare-haren 'yan ta'addan, sannan an shawarci jama'a da su tabbata su na yin taka tsan-tsan idan su na tafiye-tafiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng