'Yan Bindiga Sun Raunata Mahaifiyar Gwamna da Kanwarsa? Yan Sanda Sun Yi Martani
- An yi ta yada wasu rahotanni cewa yan bindiga sun kai mummunan hari kan mahaifiyar Gwamna Agbu Kefas na Taraba da kanwarsa
- Rahotannin suka ce yayin harin da aka kai a hanyar Wukari-Kente, an raunata su inda suke asibiti domin karbar kulawa
- Sai dai wani babban jami'in gwamnati ya musanta labarin cewa an raunata mahaifiyar Gwamna da kuma kanwarsa a harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Taraba - Rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba ta tabbatar da harin da aka kai kan hanyar Wukari-Kente.
Rundunar ta ce tabbas an kai harin a jiya Alhamis 5 ga watan Disambar 2024 wanda ake zargin ya shafi iyalan gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas.
Jami'i ya musanta raunata mahaifiyar Gwamna
An yi ta yada rahotanni cewa harin ya rutsa da mahaifiyar gwamnan da ‘yar uwarsa mai suna Atsi Kefas a hanyar da ke karamar hukumar Wukari, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake magana a kan lamarin, Shugaban karamar hukumar Wukari, Dauda Samaila Agbu ya ce Atsi Kefas ta samu raunuka sakamakon harbin bindiga.
Ya ce tana cigaba da karɓar magani a asibitin koyarwa na Tarayya da ke Wukari kafin a dauke ta zuwa Abuja domin samun karin kulawa, cewar Daily Post.
Sai dai wani babban jami’in gwamnati ya musanta rahoton da aka wallafa a kafafen sada zumunta a cikin wani sakon WhatsApp inda ya ce ba shi da tushe.
"Labarin da ke yawo cewa an kai hari kan mahaifiyar Gwamna Kefas da kanwarsa a kan hanyar Wukari-Kente ba gaskiya ba ne."
- Cewar jami'in gwamnati
Yan sanda sun yi magana kan harin Taraba
Da yake magana a yau Juma’a 6 ga watan Disambar 2024 a Jalingo, kakakin rundunar 'yan sanda, SP Abdullahi Usman ya tabbatar da aukuwar harin.
Sai dai ya ce ba a tabbatar da cewa mahaifiyar Gwamna Agbu Kefas, Jumai Kefas da 'yar uwarsa suna cikin wadanda abin ya shafa ba.
SP Usman ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatarwa jama’a cewa za su kama wadanda suka aikata laifin.
Yan bindiga sun hallaka manomi a Taraba
Kun ji cewa yan bindiga sun yi rashin imani a jihar Taraba inda sun hallaka wani babban manomi da bai san hawa ba kuma bai san sauka ba.
Tsagerun sun kuma yi awon gaba da wasu mamona shida a ƙauyen Garbatau da ke ƙaramar hukumar Bali ta jihar Taraba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng