Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muyideen Bello Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci ɗan asalin Ibadan a jihar Oyo, Sheiƙh Muyideen Bello rasuwa yana da shekara 84 a duniya
- Malamin dai ya shajara wajen wa'azi da jan hankalin al'umma su bi koyarwar addinin Musulunci, wanda hakan ya sa zama abin girmamawa
- Sheikh Akewugbagold Taofeeq ya tabbatar da rasuwar ranar Juma'a, 6 ga watan Disamba, ya yi addu'ar Allah ya jiƙansa ya masa rahama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Fitaccen malamin addinin Musulunci a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, Sheikh Muyideen Ajani Bello ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin ya kasance babban malami mai wa'azi wanda ya shahara kuma mutane na girmama shi a yankin Yarbawa.
An tabbatar da rasuwar Sheikh Muyideen
Ɗaya daga cikin malaman Musulunci a Oyo, Sheikh Akewugbagold Taofeeq ne ya tabbatar da rasuwar a wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Muyideen Bello, wanda aka haifa a shekarar 1940 a garin Ibadan ta jihar Oyo, ya shahara wajen koyarwa a addinin musulunci.
Da yake tabbatar da rasuwar malamin, Sheikh Akewugbagold Taofeeq ya ce:
"Yau tana ɗaya daga cikin ranakun bakin ciki a rayuwata, ubanmu kuma abin koyi a wurina ya koma ga mahaliccinsa.
"Sulthonul Wahizeen na kasar Yarbawa Sheikh muhyideen AJANI BELLO, Allah ya jikanka da rahama. Allah ya sa ka a gidan Aljannatul Furdausi."
Sheikh Muyideen ya yi wa Musulunci hidima
A watan Afrilu 2024, majalisar koli ta malaman Musulunci a Kudu maso Yammacin Najeriya ta naɗa shi sarautar "Sulthonil Wahizeen" (Sarkin masu wa'azi) na kasar Yarabawa.
Marigayi Sheikh Muyideen ya yi wa’azuzzuka da muhadara a wurare daban-daban, inda yake yawan jan hankalin jama’a kan bin tafarkin Musulunci.
Shugaban ƙungiyar JNI ya rasu a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa malamin Musulunci kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), Jafaru Maƙarfi ya riga mu gidan gaskiya a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa a lokacin rayuwarsa, marigayin ya riƙe kujerar kwamishina a tsohuwar jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng