"Kudirin Haraji Ya Bankado Gazawar Arewa," Tsohon dan Takarar Shugaban Kasa Ya Magantu
- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu J B Garba ya shawarci gwamnonin Arewa a kan su farka daga barcin da ake yi
- Ya bayyana cewa kudirin harajin Bola Tinubu ya bankado gazawar da tattalin arzikin shiyyar ya ke ciki na tabarbarewa
- Adamu Garba ya bayyana cewa ko an tabbatar da kudirin harajin ko akasin haka, dole gwamnonin shiyyar su dauki matakai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Adamu J.B. Garba, ya yi kira ga gwamnonin Arewacin Najeriya da su gaggauta mai da hankali kan bunkasa tattalin arzikin yankin.
Ya bayar da shawarar ne bayan abin da ya ce kudirin harajin Bola Tinubu ya tono na gazawar shiyyar Arewacin kasar nan, musamman ta fuskar tattalin arzki.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon dan takarar ya bayyana cewa akwai kalubale iri-iri da kudirin haraji ya fito da su fili, wanda da ke boye a shiyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shawarci gwamnoni ganin kudirin haraji
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya shawarci gwamnonin Arewa su gaggauta koma wa gonakinsu domin cicciba tattalin arzikin shiyyar.
Ya kara da cewa haka kuma akwai bukatar su rungumi harkar masana'antu, ganin yadda shiyyar ke da albarkatun kasa da cigaban shiyyar.
Kudirin Tinubu ya bankado matsalar Arewa
Adamu Garba ya bayyana cewa ko da gwamnati ba ta tabbatar da kudirin harajin Tinubu ba, batun ya bankado matsalolin da shiyyar ke ciki.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya nuna cewa halin da tattalin arzikin shiyyar Arewa ya nuna cewa shiyyar ta durkushe kuma dole a farka.
Kudurin haraji ya kawo sabani a majalisa
A wani labarin. mun ruwaito cewa batun kudirin harajin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ya jawo sabanin ra'ayi a majalisar dattawan kasar nan bayan samun mabambantan bayanai.
A baya, mataimakin shugaban majalisar, Barau I Jibrin ya ce an dakatar da kudirin har sai an kammala zama a kan kudirin, amma Sanata Godwill Akpabio ya ce ba za a jingine ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng