An Kashe 'Yan Bindigar da Suka Daure Babban Ma'aikaci a Cikin Rami

An Kashe 'Yan Bindigar da Suka Daure Babban Ma'aikaci a Cikin Rami

  • 'Yan sanda sun hallaka masu garkuwa da mutane uku yayin musayar wuta a maboyar su a jihar Akwa Ibom
  • Jami'ai sun ceto wani lauya, Barista Emmanuel Ubengama, tare da 'yar uwarsa daga hannun masu garkuwar
  • 'Yan sanda sun bayyana cewa suna ci gaba da kokarin cafke wadanda suka tsere domin gurfanar da su a gaban alkali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Akwa Ibom - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom sun samu nasarar hallaka masu garkuwa da mutane uku yayin da suka yi musayar wuta.

Rahotanni na nuni da cewa an fafata ne da miyagun a maboyar su a karamar hukumar Abak a yau Alhamis.

Akwa Ibom
An kashe 'yan bindiga 3 a Akwa Ibom. Hoto: Legit
Asali: Original

Leadership ta wallafa cewa 'yan sanda sun ceto wani lauya mai suna Emmanuel Ubengama, wanda darakta ne a ma’aikatar shari’a tare da ‘yar uwarsa da aka sace ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Bayan fafutukar shekaru 22: Kotu ta ba malamin da aka kora a aiki nasara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar ‘yan sanda, ASP Timfon John, ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da cewa suna ci gaba da farautar sauran miyagun da suka tsere.

'Yan bindiga sun daure ma'aikaci a rami

Masu garkuwa da mutane sun yi wa Barista Ubengama da 'yar uwarsa kwanton bauna a hanyar Abak-Ikot Abasi yayin da suke dawowa gida.

Bayan haka, miyagun sun kaisu maboyarsu da ke Ikot Ukpong, inda suka daure su a wani rami na musamman.

Rahotanni sun nuna cewa iyalan Barista Ubengama sun sanar da 'yan sanda nan take, inda kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Joseph Eribo, ya tura jami’ai domin su ceto su.

Jami'ai sun yi musayar wuta da 'yan bindiga

Jami’an rundunar sun yi musayar wuta mai zafi da miyagun a maboyarsu da ke Ikot Ukpong kuma an kashe masu garkuwa da mutane uku, yayin da wasu suka tsere daga wurin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace kansila tsakar dare, sun bi gida gida suna daukar mutane

Bayan fafatawar, jami’an tsaron sun shiga maboyar, inda suka gano wadanda aka yi garkuwa da su a cikin wani rami kuma nan take suka ceto su.

ASP Timfon John ta bayyana cewa rundunar tana da kyakkyawan shirin magance duk wasu laifuffuka, musamman a lokacin bikin Kirsimeti da ke tunkarowa.

An kama dan damfara a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane miliyoyin Naira.

'Yan sanda sun samu matashin mai suna Bishir Abdullahi da katunan ATM guda 14 da ya ke amfani da su wajen damfarar mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng