Gwamna a Arewa Ya Cika Alkawari, Ya Fara Biyan Ma'aikatan Jiharsa Albashin N70,500
- Gwamna Abdullahi Sule ya tabbatar da cewa ya fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,500 ga ma'aikatan jihar Nasarawa
- Gwamnan ya bayyana cewa jiharsa a halin yanzu ba za ta iya yin karin kudin da zai nunka albashin manyan ma’aikata ba
- Duk da ma'aikata sun shiga yajin aiki, Nasarawa na cikin jihohin da suka cika alkawarin fara biyan sabon albashi da karin girma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nasarawa - Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya tabbatar da fara biyan sabon albashi na Naira 70,500 ga ma’aikatan jihar kamar yadda ya yi alkawari.
Gwamna Sule ya kuma yi tsokaci kan bukatar kungiyoyin kwadago ta jihar na nunka albashin ma'aikatan da ke daukar sama da N70,000 a wata.
Gwamnan Nasarawa ya fara biyan albashin N70500
Gwamnan ya yi magana ne a wani shirin Arise TV a ranar Laraba inda ya ƙaryata batun cewa jiharsa ba ta fara biyan sabon albashi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Sule ya tabbatar da cewa ma’aikatan jihar ba su shiga yajin aiki saboda biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba, sai don don wata bukata tasu.
Ya ce jihar ba za ta iya nunka albashin ma'aikatan da suke karbar fiye da N70,500 ba kamar yadda 'yan kwadago suka bukata saboda rashin kudi.
Gwamnan Nasarawa ya nemi hadin kan ma'aikata
Gwamnan ya roƙi fahimtar ma’aikata, yana mai cewa jihar Nasarawa na cikin jihohin da suka cika dukkanin alƙawuran karin girma ga ma’aikata.
Ya ce tun hawansu mulki, an aiwatar da karin girma na ma’aikatan kananan hukumomi har zuwa Yuli, inda ya biya karin girman ma'aikatan jihar har zuwa Disambar 2023.
"Mun biya dukkan karin girman da ake bin mu. Mun gama da su gaba ɗaya," inji Gwamna Sule, yana mai jaddada cigaban da aka samu kan walwalar ma'aikatan jihar.
Gwamna ya shirya fara biyan sabon albashi
Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya shaidawa ma'aikatan jiharsa cewa ya kammala shirin fara biyansu sabon mafi karancin albashi.
Gwamna Sule ya shaidawa ma'aikatan cewa tuni ya gama shirin fara biyansu N70,000 bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaɓa hannu a dokar albashin.
Asali: Legit.ng