DHQ Ta Bayyana Nasarorin da Sojoji Suka Samu kan 'Yan Ta'adda a cikin Shekara 1
- Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ba da bayanai kan nasarorin da dakarun sojojin Najeriya suka samu kan ƴan ta'adda
- Daraktan yaɗa labarai na DHQ ya bayyana cewa sojojin sun hallaka ƴan ta'adda guda 8,034 a cikin shekara ɗaya a sassan daban-daban na ƙasar nan
- Manjo Janar Edward Buba ya ƙara da cewa an cafke wasu ƴan ta'adda da dama yayin da aka kuɓutar da mutane 6,376 da suka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojoji a sassa daban-daban na ƙasar nan, sun hallaka ƴan ta'adda 8,034 a cikin shekara ɗaya.
DHQ ta bayyana cewa dakarun sojojin sun kuma cafke wasu ƴan ta'adda 11,623 tare da kuɓutar da mutane 6,376 da aka yi garkuwa da su tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2024.
Sojoji sun samu nasarori kan ƴan ta'adda
Darakta mai kula da harkokin yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manjo Janar Edward Buba ya ce sojojin sun kuma ƙwato makamai 8,216, alburusai 211,459 da kuma ɗanyen mai da aka sace wanda kuɗinsa ya kai N57,052,218,551.00 a tsakanin wannan lokacin.
Edward Buba ya ce kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK47 guda 4,053, bindigogin ƙirar guda 1,123, ƙananan bindigu guda 731 da manyan bindigogi guda 240.
Sojoji sun matsa lamba kan ƴan ta'adda
Daraktan yaɗa labaran ya tabbatar da cewa sojoji na ci gaba da matsa lamba ga ƴan ta'adda wajen gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban na ƙasar nan.
"Sojoji ta waɗannan ayyuka, suna ƙara samar da yanayin da ƴan ta'adda ba za su iya yin ta'addanci ko cutar da mutane ba."
"Rundunar soji na ci gaba da nazarin hanyoyin da za a inganta ayyukanta domin tabbatar da tsaron lafiyar ƴan ƙasa"
- Manjo Janar Edward Buba
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya masu yaƙi da matsalar rashin tsaro sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda 135, a cikin sati ɗaya.
Jami'an tsaron sun kuma cafke mutane 185 da ake zargi, tare da kuɓutar da mutane 129 da aka yi garkuwa da su sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng