Lokaci Ya Yi: Shugaban Okuama Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Hannun Sojoji

Lokaci Ya Yi: Shugaban Okuama Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Hannun Sojoji

  • Watanni uku bayan kama shi, shugaban Okuama da ke karamar hukumar Ughelli a jihar Delta, Pa James Oghoroko ya mutu a hannun sojoji
  • Rahotanni sun nuna cewa shugabannin garin ne suka sanar da hakan a wurin wani zama da suka yi a jihar Delta
  • Sojoji sun kama mamacin ne tare da wasu manya a garin biyo bayan kisan gillar da wasu tsagerun matasa suka yi wa dakarun soji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta - Rahotanni sun nuna cewa shugaban al’ummar garin Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta kudu a jihar Delta, Pa James Oghoroko ya mutu.

Ana zargin cewa shugaban Okuama ya rasa rayuwarsa ne sakamakon azabtarwa a hannun dakarun sojojin Najeriya.

Pa James Oghoroko.
Babban shugaban al'ummar Okuama, Pa James Oghoroko ya mutu a tsare a hannun sojoji Hoto: @Oasis_ngMag
Asali: Twitter

Oghoroko na daya daga cikin shugabannin Okuama da sojojin Najeriya suka kama tun watan Agustan 2024, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Zanga zangar tsofaffin sojoji ta haifar da ɗa mai ido, gwamnati ta fara biyan bukatunsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa sojoji suka kama shugaban Okuama?

Sojojin sun kama su ne biyo bayan kisan gillar da ake zargin wasu gurɓatattun matasan garin sun yi wa dakarun sojojin da aka tura wani aiki a Okuama.

Hakan ya sa sojoji suka kama shugaban Okuama, Marigayi Oghoroko trae da Farfesa Arthur Ekpekpo, Cif Belvis Adogbo, Dennis Okugbaye, Pa Anthony Ahwemuria da Misis Rita Akata.

Yadda aka samu labarin mutuwarsa

Shugabannin Okuama ne suka bayyana labarin rasuwarsa a wurin wani taron gaggawa da suka gudanar a cikin garin.

Sun ƙara da cewa Pa Dennis Okugbaye, wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda ke tsare, shi ma yana cikin mummunan yanayi a hannun jami'an sojoji.

An ce Oghoroko ya mutu ne a ranar Laraba, 4 ga watan Disamba a tsare a hannun sojoji ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba tun bayan kama shi a watan Agusta.

Lauyan Okuama ya yi tir da lamarin

Kara karanta wannan

TCN zai magance matsalolin wutar lantarki, an fara inganta manyan tashoshi 3

Babban lauyan Okuama, Olorogun Albert Akpomudje SAN, ya ce zai gana da ‘yan uwan mamacin da tawagarsa domin yanke matakin da ya kamata a dauka na gaba.

Ya bayyana wannan rashi a matsayin abu mai matuƙar tada hankali musamman ga makusantansa.

Gwamnan Ondo na farko ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Ondo na farko a tarihi, Kyaftin Ita David Ikpeme ya kwanta dama yana da shekaru 89 da haihuwa.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi alhinin wannan rashi tare da miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan arzikin marigayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262