Bayan Umarnin Majalisa, CBN Ya Yi Bayanin Shirin Kashe N50bn a Sallamar Ma'aikata
- Babban bankin kasar nan (CBN), ya kare shirinsa na biyan N50bn ga ma'aikata 1000 da ya ce sun shirya ajiye aiki
- Bankin ya yi martani ga majalisar wakilai, bayan an umarce shi da ya sanya wa shirin sallamar ma'aikatan wakafi
- A sanarwar da jami'ar hulda da jama'a ta CBN, Hakama Ali ta fitar, ta ce batun ajiye aiki ba tilas aka yi wa kowane ma'aikaci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Babban bankin kasa (CBN) ya fayyace wa majalisa shirinsa na ‘Early Exit Package’, wanda ya jawo surutu saboda yawan ma'aikatan da za su bar aiki.
Bankin CBN da ya bayyana cewa zai kashe akalla N50bn domin sallamar ma’aikatansa guda 1000, inda za su yi ritaya da wuri.
Premium Times ta ruwaito cewa a sanarwar da daraktar hulda da jama’a ta bankin, Hakama Ali, ta fitar, ta ce an fito da shirin ne domin karfafawa ma’aikatanta gwiwa domin cigaba da sana’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin CBN ga majalisa kan sallamar ma'aikata
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa babban bankin kasa (CBN), ya karyata rahoton cewa ya na shirin tilastwa wasu daga cikin ma'aikatansa yin ritaya daga aiki.
Ya kuma kara da cewa batun biyan ma'aikatan da su ka yi ra'ayin ajiye aiki N50bn a matsayin kudin sallama, batu ne na cikin gida da ba ya bukatar katsalandan.
Yadda CBN ya ke shirin sallamar ma'aikata
Daraktar hulda da jama'a ta CBN, Hakama Ali ta bayyana cewa hukumar CBN ta ga dacewar yi wa ma'aikatan da ke son ajiye aiki sallama mai kauri.
Ta bayyana cewa dama a kan yi irin wannan sallama ga manyan ma'aikatan bankin, kuma an dauki aniyar gwangwaje sauran ma'aikata ne bayan kiraye-kiraye daga kungiyoyinsu.
Shirin sallamar ma'aikatan CBN ya fusata majalisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilan kasar nan ta umarci babban bankin kasa (CBN), da ya dakatar da shirin da ya ke na sallamar ma'aikatansa har su 1,000 daga aiki.
'Dan majalisa daga Ebonyi, Hon Kama Nkemkama ne ya gabatar da kudirin da ke kalubalantar shirin, kuma tuni aka kafa kwamitin da zai binciki N50bn da CBN ya ce zai kashe a sallamar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng