Gwamnan Legas Ya Yi Magana kan Kudirin Harajin Tinubu, Ya Maida Martani ga Zulum
- A ƙarshe gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya faɗi matsayarsa kan sabon kudirin harajin shugaba Bola Tinubu
- Gwamna Sanwo-Olu ya musanta cewa jihar Legas ce za ta fi amfana da sauya fasalin harajin, inda ya ce zargin ba gaskiya ba ne
- Ya bukaci masu sukar kudirin a wasu sassan kasar nan su koma su sake karanta duk abin da ke kunshe a ciki kuma su fahimta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya bayyana goyon baya ga kudirorin sake fasalin harajin da gwamnatin tarayya ta gabatar a majalisa.
Gwamna Sanwo-Olu ya ce jihar Legas ba ta da matsala da sabon tsarin harajin na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Babajide Sanwo-Olu ya faɗi haka ne yayin wata hira a wurin taron zuba jari a Afirka 2024 wanda ya gudana a ƙasar Morocco, kamar yadda Vanguard ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Legas ya goyi bayan kudirin haraji
Ya jaddada cewa akwai buƙatar sauya tsarin harajin duk da sukar da wasu ɓangarorin ƙasar nan ke yi kan kudirorin dokar guda huɗu.
Gwamnan Legas ya ce:
"Ba za mu iya kawo sauyi ba idan ba a canza fasalin haraji ba, ina rokon waɗanda suka ɗauki zafi, su zauna su fahimci abin da ke ƙunshe a kudirin sosai kafin su yanke hukunci."
Gwamna Sanwo-Olu ya musanta ikirarin Zulum
Gwamnan Legas ya kuma maida martani da Gwamna Babagana Zulum na Borno da wasu ƴan Arewa da suka yi ikirarin jihar ce za ta fi kowa amfana da kudirin.
Babajide Sanwo-Olu ya ce ko kaɗan wannan zargin ba gaskiya ba ne domin akwai wuraren da jihar ce sauyin zai taɓa.
"Na ga wasu maganganu cewa Legas ce za ta fi amfana da tsarin, wannan ba gaskiya ba ne, a zahiri akwai wuraren da mu abin zai shafa to amma idan muka sa ma'auni, kudirin ci gaba ne."
"Dukkanmu za mu amfana, idan muka duba za mu ga akwai bukatar kowa ya ƙara himma don cin gajiyar sababbin kudirorin, ba abu ne mai sauƙi ba, sai ka yi aiki," in ji shi.
Haraji: Kwamitin Majalisa zai gana da AGF
Rahoto ya gabata cewa bayan Majalisar dattawa ta jingine kudirorin haraji, kwamitin da ta kafa ya shirya zama da Antoni Janar na ƙasa watau AGF.
Ana sa ran wannan taro da za su yi zai maida hankali ne kan wuraren da ƴan Najeriya ke kuka da su a sababbin kudirorin gyara haraji a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng