Kudirin Haraji: Gwamnatin Tinubu Za Ta Rika Karbar Haraji a Kudin Gado?
- Dan majalisar tarayya Leke Abejide ya ce siyasa da addini suna daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar kudirin gyaran haraji
- Legit ta ruwaito cewa an samu rashin amincewa daga Arewacin Najeriya kan kudirin haraji da Bola Ahmed Tinubu ya tura majalisa
- Wasu 'yan Arewa suna tunanin kudirin ya ci karo da dokar gado a Musulunci, inda suke zargin za a fara cire haraji daga gado
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT Abuja - 'Dan majalisa mai wakiltar mazabar Yagba a jihar Kogi, Leke Abejide, ya bayyana cewa an saka siyasa da addini a tattaunawar da ake a kan kudirin gyaran haraji.
Hon. Leke Abejide ya ce ya shafe lokaci mai tsawo a Kano kuma Hausawa da dama sun mika masa korafi a kan kudirin.
Dan majalisar ya fadi haka ne a cikin wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba a gidan talabijin din Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin haraji da rabon gadon Musulunci
Hon. Abejide ya bayyana cewa wasu sun yi zargin cewa kudirin gyaran harajin zai bukaci mutane su fara biyan kashi 24% cikin dukiyar gadonsu.
Legit ta ruwaito cewa dan majalisar ya ce masu zargin na cewa sashe na hudu a babi na daya na kudirin yana da sabani da dokar gadon Musulunci.
Matsayar Hon. Abejide kan kudirin haraji
Duk da zarge-zargen da ake yi, Abejide ya bayyana cewa bai ga wani abu a cikin kudirin da ya nuna cewa zai yi tasiri kan gado kamar yadda ake zargi ba.
Ya yi nuni da cewa masu adawa da kudirin suna amfani da wannan batun ne domin tayar da kura, amma har yanzu babu cikakken bayani da ke tabbatar da zargin.
A karshe, Hon. Abejide ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya gayyaci malamai domin bayyana musu cewa kudirin ba ya karo da dokar rabon gado ta Musulunci.
Majalisa ta dakatar da kudirin haraji
A wani rahoton, kun ji cewa majalisa ta dakatar da tattauna kudirin haraji saboda yawan korafi da aka samu a kansa.
Bayan haka, majalisar ta kafa kwamiti da zai zauna da ma'aikatar shari'a domin warware abubuwan da suka tayar da kura kan kudirin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng