Tsofaffin Sojoji Sun Rufe Ma'aikatar Kudi a Abuja, Sun Fadi Bukatunsu
- Tsofaffin sojojin da suka yi ritaya sun rufe ma'aikatar kuɗi da ke Abuja a safiyar ranar Alhamis, 5 ga watan Disamban 2024
- Wadannan dattawan sun nuna damuwarsu kan yadda gwamnatin tarayya ta gaza biyansu haƙƙokinsu har na tsawon watanni
- Tsofaffin sojojin dai na neman a biya su kuɗaɗensu da suka shafi ƙarin albashi da wasu alawus-alawus da ya kamata a ce suna samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wasu daga cikin tsofaffin sojojin Najeriya da suka yi ritaya a ƙarƙashin gamayyar ƙungiyar ƴan fansho na soja a Abuja, sun rufe ma’aikatar kuɗi ta tarayya a safiyar ranar Alhamis.
Tsofaffin sojojin sun kulle ma'aikatar kuɗin ne saboda ƙin biyan su ƙarin albashi na kaso 20% zuwa 28% daga watan Janairu zuwa watan Nuwamban 2024.
Tsofaffin sojojin waɗanda da suka yi ritaya da suka fito daga ƙungiyoyi daban-daban sun koka da yadda gwamnatin tarayya ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanne buƙatu suke so a biya musu?
Buƙatun sojojin sun haɗa da biyan kuɗaɗen tallafi daga watan Oktoba 2023 zuwa Nuwamban 2024 da ƙarin N32,000 da aka yi musu a kuɗin fansho.
Sauran su ne biyan kuɗaɗen alawus na SDA a dunƙule da dawo da kuɗaɗen da aka cire na sojojin da ke da rashin lafiya da sauransu.
Tsofaffin sojoji sun yi zanga-zanga a Abuja
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ko a ranar Laraba, sai da tsofaffin sojojin suka gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin ma'aikatar kuɗin.
Shugaban ƙungiyar Anthony Agbas, ya koka kan yadda aka bar su cikin wahala a tsawon shekaru, ba tare da haƙƙoƙinsu ba.
"An gaya mana cewa an daɗe da amincewa a fitar da kuɗaɗen, amma har yanzu ba a ba mu komai ba."
- Anthony Agbas
Rundunar sojoji ta cafke wasu jami'ai
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta nuna fushinta kan cin zarafin wasu fararen hula da wasu jami'anta suka yi a jihar Legas.
Ta bayyana cewa ta gudanar da bincike kan lamarin da ya auku kuma za a ɗauki matakin da ya dace a kan jami'an sojojin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng