Kudirin Harajin Tinubu: Kwamitin Majalisa Zai Zauna da Babban Lauyan Gwamnati

Kudirin Harajin Tinubu: Kwamitin Majalisa Zai Zauna da Babban Lauyan Gwamnati

  • Kwamitin da majalisar dattawa ta kafa domin duba matsalolin da ake kuka da su a kudirin haraji zai fara aiki
  • Ana sa ran kwamitin zai fara ganawa da babban lauya na kasa, Lateef Fagbemi SAN domin warware matsalolin
  • Amma an samu rahotannincewa Fagbemi ba ya cikin kasar nan, lamarin da kwamitin ya ce ba zai hana zama ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta dakatar da cigaba da muhawara a kan kudirin harajin Tinubu, bayan sukar da ake yi wa dokar daga fannoni daban-daban.

Majalisar ta kuma umurci kwamitinta na kudi da ya dakatar da duk wani aiki na sauraron ra'ayin jama'a har sai an warware korafe-korafen mutane.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji ya kawo sabani a majalisa, Barau da Akpabio sun saba

Barau
Kwamitin majalisa zai zauna da gwamnati kan batun kudirin haraji Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Sanata Barau I. Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa an kafa kwamiti da zai yi aiki da bangaren zartarwa domin magance koken jama'a dangane da kudirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haraji: Kwamitin majalisa zai gana da gwamnati

Jaridar Punch ta wallafa cewa kwamitin da majalisar dattawa ta kafa domin ganawa da bangaren zartarwa zai zauna da babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi.

Sanata Barau I Jibrin da ya tabbatar da haka ya ce;

"A gobe (Alhamis), kwamitin da majalisar dattawa ta kafa zai gana da babban lauyan gwamnati domin tattauna wadannan batutuwan."

Kudirin haraji: Babban lauya ba ya kasa

Rahotanni sun bayyana cewa ba lallai ne Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi ya samu halartar zaman farko tsakanin ofishinsa da kwamitin majalisa a kan kudirin ba.

Shugaban kwamitin majalisa a kan kudirin, Abba Moro, ya ce watakila ba za su ganin da Lateef Fagbemi SAN ba, amma ‘yan majalisar za su gana.

Kara karanta wannan

Matasan N-Power na jiran bashinsu, gobara ta laƙume ma'ajiyar NSIPA, kaya sun kone

“Tun da aka ce babban lauyan ya na wajen ƙasar na , kuma kamar yadda ka fada, watakila wannan taro ba zai gudana (da babban lauya) ba.”

'Dan majalisa ya nemi afuwar na'am da kudirin haraji

A wani labarin, kun ji cewa dan majalisa mai wakiltar Kuru/Bebeji, Hon. AbdulMumin Kofa ya nemi afkuwar mutanen da ya ke wakilta da Arewacin kasar nan.

Ya nemi tafiyar jama'a ne bayan an sha jinsa ya na bayyana goyon baya ga kudirin harajin shugaban kasa duk da yadda ake zargin zai cutar da Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.