Dalilin da Ya Saka Majalisa Dakatar da Kudirin Harajin Shugaba Tinubu

Dalilin da Ya Saka Majalisa Dakatar da Kudirin Harajin Shugaba Tinubu

  • Majalisar dattawa ta dakatar da duba kudirin gyaran haraji da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar saboda matsin lamba
  • Gwamnoni, dattawan Arewa da majalisar tattalin arziki ta kasa sun bukaci karin shawarwari kafin ci gaba da aikin kudirin
  • Masana da masu sharhi a kan al'amuran yau da kullum sun bayyana wasu abubuwa a matsayin dalilin dakatar da kudirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta dakatar da kudirin gyaran haraji da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika mata.

Matakin ya biyo bayan matsin lamba daga 'yan siyasa, dattawan Arewa da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya.

Majalisa
Abin da ya sa aka dakatar da kudirin haraji a majalisa. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a yau Alhamis ne kwamitin majalisar dattawa da jami'an gwamnatin tarayya za su zauna kan kudirin.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji ya kawo sabani a majalisa, Barau da Akpabio sun saba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin dakatar da kudirin haraji a majalisa

Rahotanni sun nuna cewa shugabanin majalisar dattawa sun gana da fadar shugaban kasa domin lalubo mafita ga matsalolin da suka taso dangane da kudirin.

Biyo bayan tattaunawarsu ne aka yanke hukuncin dakatar da kudirin domin a zauna a warware abubuwan da suka tayar da kura.

Tasirin Arewa kan dakatar da kudirin haraji

Rahotanni sun nuna cewa yawan adawar da kudirin ya fuskanta daga Arewa ya taka rawa wajen dakatar da shi. Sanata Ali Ndume ya jagoranci adawa da kudirin a majalisa.

Haka zalika, gwamnonin Borno da Nasarawa tare da dattawan Arewa da majalisar tattalin arziki ta kasa, sun bukaci karin shawarwari da gyara kan kudirin kafin a yanke hukunci.

Kudirin haraji: Kwamitin majalisa zai zauna

Majalisar dattawa ta kafa kwamitin mutum 10 domin tattaunawa da ministan shari’a kan yadda za a magance matsalolin kudirin.

Kara karanta wannan

Kudirin Haraji: Gwamnatin Tinubu za ta rika karbar haraji a kudin gado?

An bayyana cewa kwamitin zai gudanar da aiki na musamman domin warware sabanin da kudirin ya jawo, tare da duba yadda za a tabbatar da ci gaban Najeriya.

Rahoton Channels Television ya nuna cewa a yau Alhamis kwamitin zai zauna domin warware matsalolin kudirin.

Kudirin haraji: Abdulmumin Jibrin ya nemi afuwa

A wani rahoton, kun ji cewa 'dan majalisa daga jihar Kano, Abdulmumini Jibrin Kofa ya nemi afuwa a kan maganar da ya yi game da kudirin haraji.

Hon. Jibrin Kofa ya ce ba zai taba goyon bayan abin da zai cutar da Arewa ba kuma bai goyi bayan kudirin dari bisa dari ba tun asali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng