Jami'an EFCC Sun Kai Samame a Gidan 'Dan El Rufai? An Gano Karin Bayanin Lamarin
- Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa jami'an EFCC sun kai samame a gidansa
- Honarabul Bello El-Rufai ya bayyana raɗe-raɗen da aka yaɗa a matsayin tsabagen ƙarya da kuma ƙoƙarin ɓata masa suna
- Ya bayyana cewa zai ɗauki matakin shari'a kan waɗanda suka yaɗa waɗannan ƙarairayin marasa tushe ballantana makama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Bello El-rufai, babban ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai, ya yi magana kan raɗe-raɗen da ake yaɗawa cewa jami'an hukumar EFCC sun kai samame a gidansa da ke Kaduna.
Bello El-Rufai ya ƙaryata raɗe-raɗin masu cewa jami'an na EFCC sun gano kuɗin ƙasashe daban-daban da aka jibge a gidansa.
Ɗan El-Rufai ya musanta samamen EFCC a gidansa
Bello El-Rufai, wanda shi ne ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa, ya musanta hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan majalisar ya bayyana zargin a matsayin ba ƙarya kawai ba, har da ƙoƙarin ɓata masa suna da kawar masa da hankali kan aikinsa na gwamnati.
Wasu rahotanni dai sun yaɗa cewa jami'an EFCC sun bankaɗo tsabar kuɗi dala miliyan 800, Naira biliyan 700, da kuma ƙwayoyi waɗanda kuɗinsu ya kai Naira tiriliyan 1 a gidansa da ke Kaduna.
Bello El-Rufai ya kare kansa
Sai dai, Bello El-Rufai ya bayyana cewa ba shi da gida a Kaduna, sai gidansu da ke Unguwar Sarki, inda a nan yake zaune kuma nan ya taso tun daga haihuwarsa.
"Mutanen mazaɓata da na ke wakilta sun san abin da zai faru idan aka albarkace ni da irin waɗannan kuɗin.
"Ga masu ɗaukar nauyin waɗannan hare-hare na jahilci, ina tabbatar muku cewa za mu ci gaba da yi wa jama’a hidima."
"Kuma za mu ci gaba da jin daɗin yadda abin ya ɓata musu rai, ba gudu da ba ja baya wajen yin wakilci na gaskiya a Kaduna ta Arewa."
- Bello El-Rufai
Ya ci gaba da cewa, tawagar lauyoyinsa za ta ɗauki matakin shari’a a kan wasu kafafen yaɗa labarai, kuma za a yi amfani da kuɗin da suka biya na ƙaryar da suka yi domin amfanin Kaduna ta Arewa.
Hukumar EFCC ta ƙwato babbar kadara
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ƙwato kadarar da ɓata irinta ba tun daga lokacin da aka kafa ta.
Alƙalin kotun tarayya, Jude Onwuegbuzie, ya bayar da hukuncin kwace katafaren gida mai fadin mita 150,500 da ke Lokogoma a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng