'Yan Sanda Sun Fadi Masu Hannu Wajen Tayar da Bama Bamai a Zamfara

'Yan Sanda Sun Fadi Masu Hannu Wajen Tayar da Bama Bamai a Zamfara

  • Rundunar ƴan sanda na reshen Zamfara ta tabbatar da tashin ababen fashewa a wasu ƙauyukan da ke jihar
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya zargi ƴan ta'addan Lakurawa da laifin dasa bama-baman
  • CP Muhammad Shehu Dalijan ya ce ƴan ta'addan na fuskantar matsin lamba daga jami'an tsaro domin su fice daga ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Rundunar ƴan sandan Zamfara ta yi magana kan bama-baman da aka tayar a wasu ƙauyukan jihar.

Rundunar ƴan sandan ta zargi sabuwar ƙungiyar ƴan ta’addan Lakurawa, da laifin tayar da bama-baman a wasu ƙauyuka biyu a gundumar Dansadau, ƙaramar hukumar Maru ta jihar.

'Yan sanda sun zargi 'yan ta'addan Lakurawa da dasa bam a Zamfara
'Yan sanda sun dora alhakin dasa bama-bamai a Zamfara kan 'yan ta'addan Lakurawa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Muhammad Shehu Dalijan ne ya bayyana mata hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

'Yan Kudu sun bi sahun masu adawa da kudirin harajin gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun zargi ƴan ta'addan Lakurawa

Da yake tabbatar da fashewar bam ɗin a ƙauyen Yar Tasha da ke kan hanyar Dansadau, CP Dalijan ya ce mutum ɗaya ne ya mutu, yayin da wasu uku suka samu raunuka daban-daban.

"Eh, an samu fashewar wani abu a kan hanyar Dansadau a safiyar yau, kuma bam ne da aka dasa a ƙarƙashin wata gada."
"Mai motar ya taka shi sannan ya fashe inda ya kashe mutum ɗaya tare da jikkata wasu mutum uku."
"Binciken farko ya nuna cewa ragowar ƴan ta’addan Lakurawa ne da sojoji suka matsa musu su bar Najeriya ne suka dasa bam ɗin."
"Yanzu haka ƴan ta’addan na ƙoƙarin gano hanyar zuwa dajin Birnin-Gwari ta cikin jihar Zamfara. Suna fuskantar matsin lamba daga jami'an tsaron Najeriya domin su fice daga ƙasar nan."

- CP Muhammad Shehu Dalijan

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma, sun hallaka ƴan ta'adda masu yawa a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun saki bama bamai a sansanin 'yan ta'adda, an hallaka myagu masu yawa

Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan ne bayan sun samu kiran gaggawa daga wajen mutanen gari da ƴan banga da ke ƙauyen Yar Galadima na ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng