‘Ka Yi Masa Afuwa’: Basarake Ya Rokawa Tsohon Gwamna Yafiyar Tinubu kan Rigimarsu

‘Ka Yi Masa Afuwa’: Basarake Ya Rokawa Tsohon Gwamna Yafiyar Tinubu kan Rigimarsu

  • An bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sansanta da tsohon yaronsa a siyasa kuma tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola
  • Sarkin Lagos, Rilwan Akiolu shi ya ya wannan roko yayin da karamin Ministan ayyuka, Bello Goronyo ya kai masa ziyara
  • Wannan na zuwa ne yayin da marigayi Alaafin na Oyo da Ooni na Ife sun yi ta kokarin sasanta su a baya amma bai yiwu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Oba na Lagos, Rilwan Akiolu ya nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu da Rauf Aregbesola ke rigima da juna.

Basaraken ya bukaci Bola Tinubu ya sasanta kuma ya yafewa tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola wanda kuma kasance yaronsa.

Basarake ya bukaci Tinubu ya yafewa tsohon gwamna
Oba na Lagos ya roki Bola Tinubu ya sasanta da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola. Hoto: @raufaregbesola, @KashimSM.
Asali: Twitter

Sarakuna sun yi kokarin sasanta Tinubu daAregbesola

Basaraken ya bayyana haka ne a fadarsa yayin karban bakwancin karamin Ministan ayyuka, Bello Goronyo, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

ACF: Kungiyar Arewa ta lashe amanta game da dakatar da shugabanta kan zaben Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a baya mutane da dama sun yi ta kokarin sasanta Tinubu da Aregbesola amma hakan bai yi tasiri ba.

A 2022, Alaafin na Oyo da Ooni na Ife sun yi zama da tsohon ministan domin shawo kan matsalar da ake tsakaninsa da Tinubu amma a banza.

Basarake ya bukaci Tinubu ya sasanta da yaronsa

Sai dai yanzu ba a sani ba ko rokon da Oba na Lagos zai yi tasiri a wurin Tinubu wanda yanzu yake da mukamin shugaban kasa.

Oba na Lagos ya fadi muhimmancin sasantawar inda ya ce sun dade suna tare a siyasance a matsayin maigida da yaronsa.

A bangarensa, Rauf Aregbesola da ke jagorantar kungiyar Omoluabi ta APC ya mayar da hankali domin kwace mulki daga PDP.

Aregbesola ya bayyana yadda kungiyar ke kokarin dawo da martabar jam'iyyar inda ya roki mambobinta su kara kaimi wurin jan hankalin al'umma.

Kara karanta wannan

2023: Na hannun daman Buhari ya yi da na sanin tallata Tinubu a Kano

Aregbesola ya gargadi Tinubu kan halin kunci

Kun ji cewa tsohon gwamna a jam'iyyar APC ya yi gargadi kan yiwuwar samun juyin-juya-hali a Najeriya saboda halin kunci da ake ciki a kasar.

Rauf Aregbesola ya koka kan yadda tattalin arziki da cigaban siyasa ke samun koma baya a kullum inda ya ce babban hatsari ne.

Tsohon gwamnan jihar Osun ya shawarci gwamnatoci su dauki matakin shawo kan matsalolin kafin juyewa zuwa wani abin daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.