Atiku Ya Dura a kan 'Yan Sanda, Ya Soki Yadda aka Kama Mai Adawa da Gwamnati

Atiku Ya Dura a kan 'Yan Sanda, Ya Soki Yadda aka Kama Mai Adawa da Gwamnati

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaicin yadda ya ce 'yan sanda ke wuce gona da iri
  • Ya bayyana haka ne a martaninsa ga kama wani mai fafutuka da nuna adawa ga wasu daga cikin manufofin gwamnati
  • Tsohon dan takarar shugaban kasar ya shawarci 'yan sanda su gaggauta sakin Dele Farotimi da ke ofishinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya caccaki yadda 'yan sanda su ka yi ram da mai fafutukar kare hakkin dan Adam a Legas.

A ranar Talata ne wasu jami'an 'yan sanda su ka dura a ofishin Dele Farotimi a Legas bisa zargin cin zarafi ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Barau ya bukaci majalisa ta mayar da sunan Yusuf Maitama a jami'ar FUE

Tinubu
Atiku ya nemi a saki mai rajin kare hakkin dan Adam Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa jami'an sun karbo izinin tafiya da Mista Farotimi, sannan su ka iza kyarsa zuwa jihar Ekiti, inda ake zarginsa da aikata laifi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya soki kama mai gwagwarmaya

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya wallafa takaicinsa a shafinsa na X, a kan yadda fadin albarkin bakin mutum ke neman zama matsala a kasar nan.

Yayin da ya ke tuna yadda aka ci zarafinsa a shekarar 2019, ya ce duk da haka bai dace 'yan sanda su rika wuce gona da iri ba a wajen amfani da ikon da kasa ta ba su saboda tsirarun mutane.

Atiku ya nemi a saki Dele Farotimi

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar nan, Atiku Abubakar, ya yi kira da a saki Dele Farotimi, wanda 'yan sanda su ka cakume shi a ofishinsa a Legas.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Sunday Abutu, ya tabbatar da kama mai fafutukar, ya bayyana cewa ana tuhumarsa ne bayan samun korafin cin zarafin da ake zarginsa da shi.

Kara karanta wannan

Sultan da shugaban CAN sun ajiye bambancin addini, sun mika bukata 1 ga Tinubu

Atiku ya magantu a kan kudirin haraji

A wani labarin, kun ji cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya ba gwamnatin Bola Ahmed Tinubu shawara a kan kudirin haraji da ya yamutsa hazo.

Tsohon dan takarar ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnatin ta saurari ra'ayoyin jama'a, sannan a daidaita kudirin ta yadda zai zo daidai da muradun jama'a da cigaban kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.