Gwamna Ya Raba Tallafin Miliyoyi domin Bunkasa Kananan Sana'o'i

Gwamna Ya Raba Tallafin Miliyoyi domin Bunkasa Kananan Sana'o'i

  • Gwamnatin jihar Neja ta raba Naira miliyan 250 ga kungiyoyin mata domin bunkasa kanana sana'o'i a Kontagora
  • Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa matan za su samu damar zama masu dogaro da kai tare da samar da aikin yi
  • Haka zalika gwamnan ya yi kira ga matan da ba sa cikin kungiyoyi su kafa nasu domin amfana da shirin tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Gwamnatin jihar Neja ta tallafawa mata da ke kungiyoyin hadin gwiwa da Naira miliyan 250 a karamar hukumar Kontagora.

Gwamna Umaru Bago ne ya sanar da tallafin yayin wata ganawa da matan kungiyoyin hadin gwiwa a yankin, ya ce wannan mataki zai taimaka wajen dogaro da kai da bunkasa tattali.

Kara karanta wannan

Bayan shawarar Kwankwaso, Jibrin Kofa ya nemi afuwa kan goyon bayan kudirin haraji

Tallafin mata
An tallafawa mata a Neja. Hoto: Bologi Ibrahim
Asali: Facebook

Legit ta tattaro rahoton ne a cikin wani sako da mai magana da yawun gwamna Umaru Bago, Bologi Ibrahim ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mata za su dogara da kansu a jihar Neja

Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa matan da aka tallafawa za su samu damar zama masu dogaro da kai da kuma masu samar da aikin yi ga wasu.

Ya kara da cewa za a yi rajistar sunayen matan da suka amfana domin samun cikakken bayani kan yadda ake amfani da tallafin, tare da tabbatar da adalci a rabon.

Gwamna Bago ya yi kira ga mata

Gwamnan ya yi kira ga matan da ba sa cikin kungiyoyin hadin gwiwa da su kafa nasu domin samun damar shiga irin wannan tallafi.

Haka kuma ya yi alkawarin kara adadin tallafin idan aka tabbatar da cewa matan sun yi amfani da kudin da aka raba ta hanya mai kyau.

Kara karanta wannan

Sububu: An yi barin jini wajen neman kujerar shugaban 'yan ta'adda da aka kashe

Kokarin gwamna Bago a kan matan Neja

Wata jami'ar gwamnatin Neja, Hauwa Mohammed Bako ta bayyana cewa gwamnan ya dauki matakai masu yawa na tallafawa mata da suka fara samar da sauye-sauye masu amfani.

Hauwa Mohammed Bako ta ce tallafi na Naira miliyan 250 na daga cikin jerin tsare-tsaren da aka kaddamar domin karfafa mata da bunkasa tattalin arzikin a jihar.

An yi karin albashi zuwa N80, 000 a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta yaba wa Gwamna Umaru Bago kan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.

Kungiyar ma’aikatan ta ce gwamna Bagoya kasance mutum mai cika alkawari kasancewar ya biya albashin N80,000 a watan Nuwamba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng