Hajjin 2023: An Biya Alhazan Kano Diyyar Sama da N375m kan Abin da Ya Faru a Saudiyya

Hajjin 2023: An Biya Alhazan Kano Diyyar Sama da N375m kan Abin da Ya Faru a Saudiyya

  • Hukumar alhazai ta jihar Kano ta maidawa mahajjatan da suka sauke farali a shekarar 2023 kuɗi sama da Naira miliyan 375
  • Shugaban hukumar, Alhaji Lamin Rabi'u ya ce Saudiyya ce ta aiko da kuɗin a matsayin diyyar ɗaukewar wutar da ya faru a Minna
  • Jami'in hulda da jama'a na hukumar jin daɗin alhazan Kano ya ce an yi tsarin da kowane alhaji zai ga kuɗinsa a asusun banki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano ta mayarwa alhazan da suka yi aikin hajji a 2023 kudi ₦375,397,680.

Alhazai 6,146 ne daga jihar Kano suka sauke farali a aikin hajjin shekarar 2023, inda kowannen su ya sami ₦61,080.

Mahajjata a Saudiyya.
Hukumar alhazan Kano ta maidawa mahajjatan da suka sauki farali a bara N375m Hoto: Inside The Haramain
Asali: Facebook

Shugaban hukumar alhazan jihar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya sanar da maida kudin a wurin taron jagororin hukumar a ofishinsa, Tribune Nigeria ta kawo.

Kara karanta wannan

Yadda gobara ta lalata kayayyakin miliyoyin naira a jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin maidawa alhazan Kano kuɗin

Lamin Rabi’u Danbappa ya ce ƙasar Saudiyya ce ta turo da kuɗin ta hannun hukumar alhazai ta ƙasa watau NAHCON a matsayin diyyar ɗaukewar wutar lantarki a Minna lokacin hajji.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Sulaiman A. Dederi, ya ce an tsara yadda za a raba kudin ga alhazai a tsanake domin tabbatar haƙƙin kowa ya isa gare shi.

Ya ce hukumar ta tsara tura kudin kai tsaye zuwa asusun kowane Alhaji domin gudun samun wata matsala.

Sannan ya tabbatarwa da jama’ar Kano cewa hukumar ta shirya tsaf wajen inganta walwala da jin dadin alhazai.

Hukumar alhazai ta koka kan rashin sayen kujeru

Alhaji Sulaiman ya ƙara da jan hankalin jami’an ofisoshin kuƙa alhazai na kananan hukumomin da su kara zage damtse wajen siyar da kujerun aikin hajji mai zuwa.

Sai dai ya nuna damuwa kan karancin cinikin kujerun hajjin, ya nemi haɗa kai da nasu ruwa da tsaki wajen ganin aikin ya tafi yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a ofishin hukumar INEC, ta yi barna mai girma

NAHCON ta fara ƙoƙarin rage kudin hajji

A wani labarin, kun ji cewa hukumar kula da alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa ta fara kokarin lalubo hanyar da za rage kuɗin hajji a 2025.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya tabbatar da cewa za su yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da cewa kuɗin hajjin mai zuwa bai kai na bara na.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262