NLC Ta Janye Yajin Aiki, Gwamna Ya Amince N80,000 Ya Zama Mafi Ƙarancin Albashi
- Ƙungiyar kwadago rashen jihar Akwa Ibom ta fasa yajin aiki bayan Gwamna Umo Eno ya amince da N80,000 a mafi karancin albashi
- Shugaban NLC, Sunny James ya ce gwamnan ya kuma kara N32,000 a kuɗin da ake ba ma'aikatan da suka yi ritaya duk wata
- James ya tabbatar da cewa gwamnatin Akwa Ibom za ta biya bashin watan Nuwamba, sannan za fara biyan sabon albashin a Disamba, 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Ƙungiyar kwadago watau NLC ta janye shirinta na tsunduma yajin aiki a jihar Kwa Ibom kan batun sabon mafi ƙarancin albashi.
NLC ta haƙura da yajin aikin ne bayan gwamnan jihar, Fasto Umo Edo ya rattaba hannu kan yarjejeniyar biyan N80,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙaranci.
Shugaban NLC na Akwa Ibom, Sunny James ne ya sanar da hakan a garin Uyo ranar Laraba, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Eno zai fara biyan albashin N80,000
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da biyan sabon mafi karancin albashi na ₦80,000 daga ranar 1 ga Nuwamba, 2024.
Bugu da kari, ya ce an kara wa wadanda suka yi ritaya N32,000 a kan fanshon da suke karɓa duk wata.
"Sakamakon cimma matsaya tsskanin gwamnatin Akwa Ibom da ƴan kwadago, muna sanar da ma'aikata cewa Gwamna Umo Eno ya ba da umarnin fara biyan mafi karanccin albashi na N80,000."
"An riga an biya albashin watan Nuwamba, 2024, gwamnati za ta biya bashin wata guda daga nan zuwa watan Fabrairu, 2025, ma'aikata za su fara ganin ƙarin albashin a watan Disambar 2024."
- Sunny James.
Kungiyar NLC ta yabawa gwamnan Akwa Ibom
Shugaban NLC ya yabawa Gwamna Eno bisa matakin da ya dauka cikin gaggawa, inda ya jaddada cewa ma’aikata za su ƙara dagewa wajen sauki nauyin da ke kansu.
Ya kara da cewa sakamakon wannan yarjejeniya da aka cimmawa, NLC ta janye yajin aikin sai baba ta gani da ta shirya shiga ranar 4 ga watan Disamba, rahoton The Nation.
NLC ta tabbatar da fara biyan albashi a Enugu
Rahoto ya gabata cewa ƴan kwadago a jihar Enugu sun tabbatar da cewa gwamna ya fara biyan sabon mafi karancin albashi tun a watan Nuwamba.
A wata sanarwar haɗin guiwa, NLC da TUC sun bayyana matsalar da aka samu bayan fara biyan sabon albashin, sun ankarar da Gwamna Peter Mbah.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng