Kwana 70 Babu Wutar Lantarki: 'Yan Kasuwar Kano Sun Yi Gangamin Sallar Alƙunuti
- Masu kanana da matsakaitan masana’antu a Dakata, karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano sun gudanar da sallar Alkuniti
- 'Yan kasuwar sun ce sun shirya addu'ar ne bayan shafe tsawon kwanaki 70 ba tare da samun wutar lantarki daga KEDCO ba
- A cewarsu, sama da 'yan kasuwa 10,000 ne rashin wutar lantarkin ya shafa kuma hakan ya janyo masu asarar miliyoyin Naira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Al'ummar da ke zaune a Dakata, karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano sun shafe kwanaki 70 kenan ba tare da wutar lantarki ba.
Rahoto ya nuna cewa kamfanin da ke samar da wuta a Kano da kewaye (KEDCO) bai kai wuta yankin Dakata ba na tsawon wadannan kwanaki.
Mutanen Kano sun yi kunutin rashin wuta
Sakamakon rashin wutar, 'yan kasuwar Dakata sun yi gangamin addu'o'i tare da yin Alkunuiti kan duk wanda ke da hannu a lamarin, a cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar 'yan kasuwar, sama da masu kananun sana'a 10,000 (SMEs) ne rashin wutar lantarkin ya jawo masu asarar miliyoyin Naira a yakin Dakata.
Sun yi Sallar Nafila tare da yi addu’ar Allah ya hukunta duk wadanda ke da hannu a halin da suke ciki.
'Yan soshiyal midiya sun yi tsokaci
@Yinkalayioye:
"Tikitin Muslim-Muslim na aiki, kuma muna son hakan."
@Corperemma_001
"Sau tari sai dai mu koma yin addu'a idan muka zabi shugabannin da ba su dace ba."
@habibb2k
"Wannan na da cikin kuskuren zabar shugabanni saboda addini, kabilanci ko son zuciya."
@AishaTafida5
"Ba ma su ga komai ba ma damar ire iren wadannan shugabannin ne za su ci gaba da zaba."
Abba zai kashe N1.7bn a gyaran wuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar zartarwar jihar Kano karkashin shugabancin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta kashe N1.7bn a gyaran wutar lantarki.
Gwamna Abba ya ce za a yi amfani da kudin wajen sayo sababbin na'urorin rarraba wutar lantarki guda 500 da za a rabasu a dukkanin kananan hukumomin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng