Jami'in Tsaro Ya Shirya Sace Kansa, Ya Nemi Fansar N50m
- Jami'an hukumar tsaron Amotekun sun yi nasarar ceto mutumin da ya sace kansa daga inda ya buya a jihar Ondo
- Matashin, mai suna Sule Gende ya shirya a sace kansa a gonar roba da ya ke yin aiki a jihar Edo da hadin bakin abokansa
- Sai dai wanda ya ke yi wa aiki sun nemi tallafin jami'an hukumar Amotekun a maimakon biyan kudin fansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ondo -Jami’an tsaron Amoekun sun cafke wani Sule Gende, wanda ke bayar da tsaro a gonar roba a Jihar Edo.
An kama mai gadin ne bisa zargin shirya sace kansa tare da neman fansar Naira miliyan 50 daga wanda ya ke yi wa aiki.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kwamandan rundunar Amotekun a Ondo, Cif Adetunji Adeleye, ne ya bayyana nasarar kamen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda jami’in tsaro ya shirya sace kansa
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a Gende domin sace shi a hanyar zuwa Edo.
Ya bayyana cewa jami’in ya tsara yadda za a “sace” shi, sannan aka kai shi wani wuri a aka boye a gidan wani abokinsa a jihar Ondo.
An kama jami'in da ya sace kansa
Wani ma’aikaci a gonar robar jihar Edo ya bayyana yadda bidiyon CCTV ya nuna yadda wasu su ka sace Gende daga cikin gonar.
Daga bisani ne mamallaka gonar su ka nemi tallafin hukumar tsaron Amotekun ta Ondo, har aka yi nasarar ‘ceto’ shi daga inda ya buya.
Jami'an tsaro sun samu bayani kan Lakurawa
A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojojin kasar nan ta samu karin bayani a kan 'yan ta'addan Lakurawa da su ka fara kafa sansani a wasu jihohin Arewa maso Gabas.
Jagoran cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, Manjo Janar Adamu Laka, bayyana cewa an gano adadin 'yan kungiyar bai wuce mutum 200 ba, kuma an fara daukar matakan murkushe su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng