Wike Ya ba 'Yan Najeriya Shawara kan Gwamnatin Bola Tinubu

Wike Ya ba 'Yan Najeriya Shawara kan Gwamnatin Bola Tinubu

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya buƙaci ƴan Najeriya sun ƙara kai zuciya nesa da gwamnatin Bola Tinubu
  • Wike ya bayyana cewa shugaban ƙasan zai kawar da yunwa tare da tunkarar matsalar rashin tsaro da ake fama da ita
  • Ministan harkokin babban birnin Abuja ya nuna ƙwarin gwiwar cewa nan ba da jinawa ba, abubuwa za su daidaita a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta kawar da yunwa sannan ta yaƙin rashin tsaro a ƙasar nan.

Nyesom Wike ya bayyana haka ne a lokacin da ya ƙaddamar da aikin titin Kabusa zuwa Takushara mai tsawon kilomita 9.8.

Wike ya bukaci a kara hakuri da gwamnatin Tinubu
Wike ya ce Tinubu zai kawo karshen yunwa Hoto: @govwike, @DOlusegun
Asali: Twitter

Ministan birnin tarayyya Abujan ya bukaci ɗan kwangilar ya bi ƙa’idoji wajen gudanar da aikin, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Kano ya fadi shirin da aka yi wa Tinubu kan kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Wike ya ba ƴan Najeriya?

Ministan ya buƙaci ƴan Najeriya musamman mazauna Abuja da su ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu, yana mai ba su tabbacin cewa abubuwa za su daidaita nan ba da daɗewa ba.

Wike ya ce gina tituna a tsakanin ƙauyuka na daga cikin alƙawuran da shugaba Tinubu ya yi wa jama’a.

A cewarsa, ingantattun hanyoyi za su taimaka wajen daƙile rashin tsaro a faɗin yankin, tare da samar da hanyoyi masu sauƙi ga manoma domin kai amfanin gonakinsu zuwa kasuwa.

Wike ya ba mutanen Abuja shawara

Wike ya bukaci mazauna babban birnin tarayya Abuja da ka da su saurari mutane masu yaɗa farfaganda, amma su yi amanna da gwamnati mai ci saboda ayyukan da take yi.

"Ka da ku saurari mutanen da ba su taɓa zuwa wajen ku ba. Ka da ku saurari mutanen da suke kawo farfaganda da alƙawuran ƙarya."
"Ku saurari mutanen da suka yi muku alƙawari kuma suka cika."

Kara karanta wannan

Ana batun kudirin haraji, Sarkin Musulmi ya ba 'yan Najeriya shawara

- Nyesom Wike

Lauya ya maka Nyesome Wike a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen lauya a Arewacin Najeriya, Abba Hikima ya jagoranci kai ƙarar ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike a gaban kotu.

Abba Hikima ya ce sun haɗa da gwamnatin Tinubu da shugaban yan sandan Najeriya, a ƙarar da su ka shigar babbar kotun tarayya da ke Abuja saboda zargin cin zarafin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng