'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malamin Addini a kan Hanya

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malamin Addini a kan Hanya

  • Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani limamin cocin Katolika a jihar Enugu da ke yankin Kudu maso Gabas na ƙasar nan
  • Miyagun sun yi garkuwa da malamin addinin kiristan ne lokacin da yake kan komawa gida bayan ya halarci wanu taro
  • Sakataren ƙungiyar fastocin cocin Katolika a yankin Kudu maso Gabas ya tabbatar da sace limamin a cikin wata sanarwa da ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Enugu - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika a jihar Enugu da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Ƴan bindigan sun yi garkuwa da malamin addinin mai suna, Gerald Ohaeri a yammacin ranar Asabar a kan babban titin Ugwogo Nike-Opi a ƙaramar hukumar Nsukka ta jihar.

'Yan bindiga sun sace malamin addini a Enugu
'Yan bindiga sun yi garkuwa limamin cocin Katolika a Enugu Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka sace malamin addinin

Sakataren ƙungiyar fastocin cocin Katolika a yankin Kudu maso Gabas, Vitalis Anusionwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Premium Times.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun saki bama bamai a sansanin 'yan ta'adda, an hallaka myagu masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Anusionwu, wanda shi ma limamin cocin Katolika ne, ya ce ƴan bindiga sun yi garkuwa da malamin addinin ne a hanyarsa ta dawowa daga Isienu bayan wani taro da aka gudanar a birnin Enugu.

"Muna neman addu’o’inku domin Allah ya sanya a gaggauta sako shi ya dawo cikinmu cikin ƙoshin lafiya."

- Vitalis Anusionwu

Ƴan sandan Enugu ba su ce komai ba

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya ɗauki kiran da aka yi masa ta waya, amma sai ya ce a tura masa saƙo ta wayarsa domin ya ba da bayani.

"Ka tura mani saƙo ne a waya domin na fahimci abin da ya faru."

- Daniel Ndukwe

Sai dai, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba.

Ƴan bindiga sun kashe fasto a Kwara

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki gwamna a Najeriya, gwamnati ta yi bayani

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka wani babban fasto, Apostle Ranti Ige-Daniel, na cocin Royal Assembly Sanctuary bayan kammala wa'azi a Kwara.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun kai hari kan malamin a kan hanyar garin Idofin zuwa Makutu lokacin da yake tare da wasu mutane uku a cikin motarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng