Hadimin Tinubu Ya Fadi Muhimmin Amfani 1 da Gyaran Haraji Zai Yiwa Yankin Arewa
- Sabon mai ba shugaban kasa shawara kan sadarwa, Daniel Bwala ya ce dokar gyaran haraji za ta amfani talakawan yankin Arewa
- Yayin da wasu ke zargin kudirin harajin zai talauta Arewa, Bwala ya ce akwai rashin fahimta kan wannan kudirin na Bola Tinubu
- Hadimin shugaban kasar ya ce akwai 'yan Arewa da suka amince da kudurin amma wasu ne ke adawa da ita saboda dalilin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Daniel Bwala, mai ba shugaban ƙasa shawara kan sadarwa, ya ce dokokin gyaran haraji za su amfani talakawan da ke a Arewacin Najeriya.
Ana ci gaba da sukar gwamatin tarayya kan wannan kudirin gyaran harajin tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya aika shi ga majalisar tarayya.
Hadimin Tinubu ya kare gyaran haraji
Bwala ya yi magana kan kudurin gyaran harajin ne a ranar Talata a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin Tinubu ya ce akasin abin da ake tunani, dokar ba za ta talauta Arewa ba, kuma mutanen Arewa da yawa suna goyon bayanta.
"Ni dan Arewa ne, kuma na damu da yadda ake yada labaran cewa dokar na nufin cutar da yankin Arewa, wanda na san ba gaskiya ba ne."
- A cewar Bwala.
Daniel Bwala ya fadi amfanin gyaran haraji
Bwala ya kara da cewa:
"Doka ce da aka tsara don rage matsalolin talauci, musamman ga talakawa a yankin Arewa."
Ya yi zargin cewa masu sukar dokar na yin hakan ne don cimma wata manufa ta siyasa ko kuma neman kulla wata yarjejeniya da Shugaba Tinubu.
Bwala ya ce akwai rashin fahimta cewa kudirin zai kawo talauci, amma akasin haka dokar ta fi karkata wajen tallafawa talakawa.
Dan majalisa ya magantu kan gyaran haraji
A wani labarin, mun ruwaito cewa dan majalisar Damboa/Gwoza/Chibok a majalisar wakilai, Hon. Ahmadu Jaha ya yi magana kan kudurin gyaran haraji.
Hon. Jaha daga jihar Borno, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya janye kudirin daga majalisa tare da yin kwaskwarima a bangarorin da suka jawo ce-ce-ku-ce.
Asali: Legit.ng