Gwamnan Borno, Zulum Ya Fadi Masu Amfana da Rikicin Boko Haram

Gwamnan Borno, Zulum Ya Fadi Masu Amfana da Rikicin Boko Haram

  • Gwamnan jihar Borno ya sake taɓo batun rikicin Boko Haram wanda ya damu musamman yankin Arewa maso Gabas
  • Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi zargin cewa akwai waɗanda ba su son rikicin ya ƙare saboda suna amfana da shi
  • Gwamna Zulum ya yi kira da a riƙa ba jami'an tsaro goyon bayan domin ganin an kawo ƙarshen matsalar a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sake yin magana kan matsalar ƴan ta'addan Boko Haram.

Mai girma Gwamna Zulum ya yi zargin cewa akwai masu amfana da rikicin na Boko Haram wanda kusan ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.

Zulum ya yi magana kan Boko Haram
Gwamna Zulum ya ce akwai wadanda ba su son rikicin Boko Haram ya kare Hoto: @govborno
Asali: Facebook

Gwamnan na jihar Borno ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaridar BBC Hausa a tsakyar makon nan.

Kara karanta wannan

Abba ya ziyarci daliban Kano a kasar Indiya, zai cigaba da daukar nauyin karatun talakawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka kasa kawo ƙarshen Boko Haram?

Gwamna Zulum ya ya bayyana cewa masu amfana da matsalar rashin tsaron da ta addabi yankin Arewa maso Gabas da Tafkin Chadi, ne suka sanya aka kasa kawo ƙarshen matsalar Boko Haram.

“A wannan tafiyar akwai waɗanda ba su son wannan yaƙin ya ƙare domin ba za su ji daɗi ba."

- Farfesa Babagana Umara Zulum.

Sai dai, gwamnan na Borno bai fito ya kira sunayen waɗanda yake nufi ba masu son ganin an ci gaba da rikicin.

Zulum ya damu kan rikicin Boko Haram

Gwamna Zulum ya ce duk da an samu ci gaba a yaƙi da matsalar tsaron, a yanzu mayaƙan na Boko Haram suna shigowa daga ƙasar Chadi.

Ya ce mayaƙan sun kwararo ne bayan an fatattako su daga Chadi, inda har ma sun jawo asarar rayukan sojojin Najeriya da dama.

Gwamnan na Borno ya ce akwai buƙatar haɗin kai tsakanin al’umma da kuma bayar da goyon baya ga jami’an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar Boko Haram a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki gwamna a Najeriya, gwamnati ta yi bayani

Gwamna Zulum ya ja kunnen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya gargaɗi shugaba Bola Tinubu kan ƙudirin haraji da aka kawo,

Gwamna Zulum ya ce duk da cewa Tinubu na da ikon aiwatar da ƙudirin haraji, amma yin hakan na iya haifar gagarumar illa ga miliyoyin ƴan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng