Mafi Karancin Albashi: Kungiyar NLC Ta Dakatar da Yajin Aiki a Kaduna, Ta Kafa Sharadi

Mafi Karancin Albashi: Kungiyar NLC Ta Dakatar da Yajin Aiki a Kaduna, Ta Kafa Sharadi

  • Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) a jihar Kaduna ta dakatar da yajin aikin da ta fara kan sabon mafi ƙarancin albashi
  • NLC ta dakatar da yajin aikin ne domin ba gwamnatin jihar damar sake duba sabon tsarin albashin da ake biyan ma'aikata
  • Shugaban NLC na jihar, ya nuna godiyarsa ga ma'aikata kan yadda suka ba da goyon baya dangane da yajin aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduna ta dakatar da yajin aikin da take yi kan rashin biyan mafi ƙarancin albashi na N72,000 ga ma’aikata.

Ƙungiyar NLC ta dakatar yajin aikin na tsawon kwanaki bakwai domin ba gwamnatin jihar damar sake duba tsarin biyan albashin, wanda aka yi watsi da shi saboda rashin daidaito.

NLC ta dakatar da yajin aiki a Kaduna
NLC ta dakatar da yajin aiki kan mafi karancin albashi a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Shugaban NLC na Kaduna, Ayuba Suleiman, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, babban birnin jihar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan Neja ya fara biyan albashin da ya fi na sauran jihohin Arewa ta Tsakiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa NLC ta dakatar da yajin aiki a Kaduna?

A cewar shugaban na NLC, sun yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bayan wata ganawa da suka yi da wakilan gwamnati a daren ranar Litinin.

"Mun gana da wakilan gwamnati inda muka amince da dakatar da yajin aikin na tsawon kwanaki bakwai domin ba su damar sake duba tsarin biyan albashin."
"Mun ƙi amincewa da biyan kuɗin saboda an cire wasu ma'aikata, an biya wasu abin da bai kai ba yayin da aka ba wasu abu mai yawa. Muna son tsarin biya na bai ɗaya wanda ya yi daidai da sabon mafi ƙarancin albashi."

- Ibrahim Suleiman

Ibrahim Suleiman ya nuna godiyarsa ga ma'aikatan jihar Kaduna kan goyon bayan da suka ba da lokacin yajin aikin.

NLC ta caccaki gwamnan jihar Ebonyi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya yi Allah-wadai da barazanar da gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ke yi ga ma’aikata.

Kara karanta wannan

Yajin aik: NLC ta yi martani ga gwamnan da ke shirin korar ma'aikata cikin kwanaki 3

Gwamnan ya fara barazana ga ma’aikatan ne bayan sun tafi yajin aikin gargadi saboda kin biyansu mafi karancin albashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng