Ana Ta Rigima kan Kudirin Haraji, Akpabio Ya Yi Barazana ga Wasu Sanatoci a Majalisa
- Yayin zaman Majalisar Dattawa a yau Talata 3 ga watan Disambar 2024, shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya gargadi wasu sanatoci
- Akpabio ya sha alwashin tube duk wani shugaban kwamiti da ya gaza yin abin da ake tsammani daga gare shi a Majalisar dattawan kasar
- Hakan na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan sabon kudirin haraji da wasu ke zargin zai yi rugu-rugu da tattalin arzikin wasu yankuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya gargadi wasu daga cikin sanatoci a Majalisar.
Akpabio ya yi barazanar tube wasu daga cikinsu musamman shugabannin kwamitoci da suka gaza tabuka wani abu.
Akpabio ya gargadi wasu sanatoci a Majalisa
Akpabio ya bayyana haka ne yayin zaman Majalisar a yau Talata 3 ga watan Disambar 2024 a Abuja, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban Majalisar ya yi wannan gargadi ne yayin amsa korafin Sanata Abdul Ningi kan kwamitin kudi.
Sanatan ya yi zargin cewa kwamitin Majalisar a bangaren kudi ya gaza gudanar da aikinsa na kula da hukumomi 92 da ke samar da haraji.
Akpabio ya koka kan yadda shugabannin hukumomi da ma'aikatu ke cigaba da kin mutunta gayyatar Majalisar.
Akpabio ya gargadi shugabannin kwamiti a Majalisa
"Idan har wani dalili ya sanya kwamiti ba su iya kula da ayyukan da aka daura musu, za mu sauya su."
"Hakan zai ba da damar kawo wasu da za su iya sauke nauyin da aka daura musu cikin sauki domin inganta martabar dimukraɗiyya."
- Godswill Akpabio
Akpabio ya bukaci dukkan kwamitcocin da su tabbatar sun rubuta rahotonsu na shekara zuwa watan Janairun 2025.
An musanta jita-jitar fadan Akpabio da Bamidele
Kun ji cewa shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ya mayar da martani kan jita-jitar rigimarsa da Godswill Akpabio.
Bamidele ya ce babu inda suka yi cacar-baki da ba hammata iska da shugaban Majalisar a ranar Laraba 20 ga watan Nuwambar 2024.
Hakan ya biyo bayan wallafa wani rahoto cewa Bamidele ya yi fada da Akpabio kan nunawa Sanatocin Kudu wariya a Majalisar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng