Lokaci Ya Yi: Tsohon Shugaban NLC Ya Mutu bayan Ƴar Hatsaniya da Ƴan Sanda
- Tsohon shugaban NLC a jihar Edo, Kwamared Kaduna Eboigbodin ya mutu bayan wata ƴar hatsaniya da ƴan sanda a Benin
- An ruwaito cewa wasu ƴan sanda ne suka tare shi, suka hana shi wucewa lamarin da ya harzuka shi ya faɗi ƙasa matacce
- Rundunar ƴan sanda ta musanta aikata laifi a lamarin, ta ce labarin da matarsa ta bayar ya saɓawa na ƙungiyoyin fararen hula
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Tsohon shugaban ƙungiyar kwadago (NLC) reshen jihar Edo, Kwamared Kaduna Eboigbodin ya riga mu gidan gaskiya.
Bayanai sun nuna cewa tsohon shugaban NLC ya mutu ne bayan wata ƴar hatsaniya ta haɗa shi da ƴan sanda a yankin Upper Sokponba a Benin.
Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa yanzu haka ƙungiyoyin fararen hula sun ba rundunar ƴan sanda sa'o'i 48 ta gano jami'an da ke da hannu kuma a hukunta su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda tsohon shugaban NLC ya mutu
An ce jami'an ƴan sandan sun tare Kwamared Eboigbodin a lokacin da ya fito tare da mai ɗakinsa a mota za su je wani wuri, suka nemi ya nuna masu takardu.
A cewar matarsa, da ƴan sanda suka ga takardunsa lafiya kalau, sai suka yi zargin cewa akwai banbanci tsakanin zanen gilashin mota da lambarsa.
Ta ce duk da bayanan da ya yi masu, ƴan sandan suka kama shi, suka kwace takardun sannan suka sa a ɗauke motarsa daga wurin.
Rahoto ya nuna cewa hatsaniya ta kaure a tsakaninsu a wurin, kwatsam sai dai gani aka yi Kwamared Kaduna Eboigbodin ya yanke jiki ya faɗi.
Matarsa da taimakon mutanen da ke wurin suka ɗauke shi zuwa aibiti amma daga zuwa likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa.
Wane mataki rundunar ƴan sanda ta ɗauka?
Shaidun gani ido sun ce jami'an ƴan sandan guduwa suka yi maimakon su ba da agaji a lokacin da mutumin ya faɗi ko motsi baya yi.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Edo ta musanta zargin aikata ba daidai ba a lamarin.
Mai magana da yawun rundunar, SP Moses Yamu ya bayyana cewa labarin da ƙungiyoyin suka bayar na abin da ya faru ya saɓawa bayanan matar marigayin.
Yan sanda sun harbi hadimin gwamna
A wani rahoton, kun ji cewa an shiga wani irin yanayi da yan sanda a jihar Osun suka harbi hadimin Gwamna Ademola Adeleke.
Yan sanda sun karbi shugaban hukumar gudanarwar tashoshin mota a jihar, Nuruddeen Iyanda da ke kulle a wurinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng