Sububu: An Yi Barin Jini wajen Neman Kujerar Shugaban 'Yan Ta'adda da Aka Kashe
- Rahotanni sun tabbatar da cewa fada ta barke tsakanin bangarorin yan ta'adda guda biyu a jihar Zamfara
- Ana hasashen an kaure da fadan bayan kisan kanin shugaban 'yan bindiga, Najaja da ake kira Dan'auta
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da neman iko tsakanin Najaja da kuma Dullu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - An yi arangama tsakanin bangarori biyu na 'yan bindiga a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma.
Fadan ya barke ne a jiya Litinin 2 ga watan Disambar 2024 inda aka yi ajalin kasurgumin dan bindiga da ake kira Dan'auta.
An hallaka kwamandan yan bindiga a Zamfara
Rahoton Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa ana rigima ne tsakanin yan ta'addan kan neman iko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana rigimar kan neman iko da kasurgumin dan bindiga da ake kira Najaja ya gaji Halilu Sububu bayan ya mutu.
Dan'auta da aka hallaka yayin arangama da Dullu ya kasance kanin Najaja da ya gaji kujerar Sububu.
Dullu ya dade yana korafi da Dan'auta ya samu dama kuma yake neman mamaye wasu wurare saboda iko da dan uwansa, Najaja yake da shi.
Rahotanni sun tabbatar cewa Dullu yana da yara akalla 400 wanda yake ganin bai dace Najaja ya gaje kujerar Sububu ba duk da karfin ikonsa.
Daukakar Najaja ya farraka bangarorin guda biyu wanda ya jawo gaba mai tsakani a tsakaninsu.
Ana fargabar kazamar fada tsakanin yan bindiga
Majiyoyi sun tabbatar da cewa ana fargabar kisan Dan'auta zai tilasta daya bangaren daukar fansa mai muni.
Masana na ganin Najaja zai dauki fansar ran Dan'auta da kuma wasu kannensa guda uku da aka hallaka da suke da tasiri a tawagarsa.
Ana hasashen cewa idan har ba shawo kan lamarin ta fannin sulhu ba, za a yi barin jini tsakanin Dullu da Najaja.
An hallaka yan bindiga a Zamfara
Kun ji cewa wasu yan bindiga da dama sun gamu da ajalinsu bayan sun je daukar fansar kisan jagoransu da aka kashe tun a watan Satumba.
Maharan sun ci karo da matsala ne a Unguwar Galadima da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara inda yan banda suka farmusu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng