Majalisa Ta Hango Matsala a Shirin CBN na Sallamar Mutum 1000, Ta Tsayawa Ma'aikata

Majalisa Ta Hango Matsala a Shirin CBN na Sallamar Mutum 1000, Ta Tsayawa Ma'aikata

  • Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya dakatar da shirinsa na yi wa ma’aikata har 1,000 ritaya
  • 'Dan majalisar daga jihar Ebonyi, Hon Kama Nkemkama ya gabatar da kudurin inda ya nuna damuwa kan rashin tsari a ritayar
  • Majalisar ta kafa kwamiti da zai binciki ritayar ma'aikatan CBN da shirin raba masu N50bn matsayin kudin sallama daga aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci CBN da ya dakatar da shirin yiwa ma’aikata 1,000 ritaya tare da biyan su kusan N50bn a matsayin kudin sallama.

Legit Hausa ta rahoto cewa CBN na shirin sallamar daraktoci da manyan ma’aikata, wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce kan wannan mataki.

Majalisar wakilai ta yi magana yayin da CBN ya shirya yiwa ma'aikata 1000 ritayar dole
Majalisar wakilai ta kafa kwamitin bincike yayin da ta hana CBN sallamar ma'aikata 1000. Hoto: @cenbank, @HouseNGR
Asali: Twitter

Majalisa ta hana ritayar ma'aikata a CBN

A zaman majalisar na Talata, an kafa kwamiti na musamman don bincikar yadda aka shirya sallamar ma’aikatan domin tabbatar da gaskiya a tsarin, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yajin aik: NLC ta yi martani ga gwamnan da ke shirin korar ma'aikata cikin kwanaki 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Kama Nkemkama, dan majalisa daga jihar Ebonyi ne ya gabatar da kudurin gaggawa kan shirin CBN na sallamar ma'aikatan da ake ganin ba a bi ka’ida ba.

Dan majalisar ya ce sallamar za ta iya haifar da matsalolin tattalin arziki, ƙaruwar rashin aikin yi, da kuma rashin jin daɗin jama’a.

An kafa kwamitin binciken shirin bankin CBN

Nkemkama ya bayyana damuwa kan yadda CBN ya ware N50bn a matsayin kudin sallamar ma'aikatan da za a yiwa ritayar, yana mai zargin cewa akwai 'lauje cikin nadi' a lamarin.

'Dan majalisar ya ce akwai bukatar bincikar yadda aka shirya fitar da kudin domin gudun karya doka da kuma amfani da kudin gwamnati ba bisa ka'ida ba.

The Cable ta rahoto shugaban majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya ba da umarnin amincewa da kudurin ta hanyar kada kuri’ar baki.

An bai wa kwamitin da aka kafa makonni huɗu domin kammala bincike da miƙa rahoto ga majalisar domin daukar mataki na gaba.

Kara karanta wannan

"Abin da ya kamata Tinubu ya yi kan gyaran haraji," Dan majalisar Arewa ya magantu

An runtuma kora a bankin CBN

A wani labarin, mun ruwaito cewa babban bankin Najeriya ya ba sama da ma'aikata 40 takardar sallama daga aiki a watan Afrilun 2024.

An ce shugaban CBN, Olayemi Cardoso ya sallami kimanin ma'aikata 67 daga aiki, a cigaba da garambawul ɗin da yake yi wa tsarin gudanarwar bankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.